Makanike Ya Ki Karbar Kudi Daga Mai Mota Bayan Ganin Hoton Peter Obi A Jikin Motar
- Wata mai goyon bayan Labour Party a Benin, jihar Edo ya sha mamaki bayan wani makanike ya ki karbar kudi bayan gyara mata mota
- Makaniken ya ki karbar kudi daga hannun matar saboda ta lika fostan Peter Obi a gaban motarta
- A wani bidiyo da ya bazu a dandalin sada zumunta, matar ta gode wa makaniken ta kuma shawarci mutane su rika kai masa gyara
Benin, Jihar Edo - Wani makanike a jihar Edo ya ki karbar kudi daga wata mai mota bayan ya gama mata gyara kawai saboda tana goyon bayan Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na Labour Party.
Matar ta tafi wurin makaniken lokacin da motarta ya samu matsala, amma ya ki karbar kudi bayan gyara mata saboda ya ga fostan Peter Obi.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Matar, cike da murna ta nadi bidiyon makaniken lokacin da ya ke aiki a motarta.
Ga abin da ta ce a bidiyon da ya bazu a dandalin sada zumunta:
"Barka da safiya, na kawo mota ta shago domin makanike ya gyara min, amma ya ga hoton Peter Obi a gaban motar kuma ya ce saboda ni 'Obidient' ce zai yi min gyara kyauta.
"Don Allah zan saka adireshin makaniken, duk wanda ya ke Benin, ku rika kawo motarku nan, mutumin kirki ne."
Da ya ke amsawa, makaniken ya ce:
"Eh, mu ne 'Obidient' na duk duniya."
Zaben 2023: Peter Obi Ya Ce Ko Ƴaƴan Cikinsa Ba Su Yarda Da Shi Idan Ya Yi Alƙawari, Mutane Sun Yi Martani
Peter Obi, dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party, LP, yana shan suka a soshiyal midiya saboda amsar da ya bada kan tambayar da aka masa game da yadda zai farfado da lantarki a Najeriya.
Mai gabatar da shirye-shirye a gidan talabijin na Arise TV ya ce wannan shine dalilin da yasa ya kamata dan takarar LP din ya fitar da manufofinsa ga kasar a rubuce don mutane su gani su yi nazari.
Amma Peter Obi ya cigaba da bayani ya bayyana yadda yayansa a gida ba su yarda da shi kuma suka dagewa sai ya nadi kalamansa a rikoda don su tunatar da shi duk lokacin da bukatan hakan ya tashi.
Asali: Legit.ng