Canji! Kalli hotunan wasu motocin alfarma da aka fara ƙerawa a Najeriya
Kamfanin kerekeren motoci na ‘Innoson Vehicle Manufacturing’, wanda shine irinsa na farko a Najeriya ya yi bajakolin wasu motoci da aka ya kera a nan gida Najeriya, kamar yadda Legit.ng ta ruwaito.
Shugaban kamfanin, mai suna Cif Innocent Ifediaso Chukwuma ya bayyana sunayen motocin da suka kera, wanda suka hada da IVM G80, IVM G40, IVM G20, da kuma kirar IVM Granite.
KU KARANTA: Rashin Kamo Shekau ba shi ne dalilin da yasa Buratai ya canza ni ba – Manjo Janar Attahiru
Wannan bajakolin basirar kere keren samfurin motocin kamfanin Innoson ya gudana ne a farfajiyar kamfanin Innoson dake garin Nnewi, jihar Abia.
Ana sa ran wannan kamfani zai taimaka wajen samar da ayykan yi ga matasan Najeriya, tare da taka muhimmiyar rawa wajen cigaban tattalin arzikin kasa a Najeriya.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sha fadin cewa muhimmin hanyar da ya kamata Najeriya ta bi wajen habbaka tattalin arzikin kasa, shi ne ta hanyar samar da dukkanin abin da yan Najeriya suke bukata a gida, ba tare da an dogara kacokan kan kayan kasashen waje ba.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng