Kotu Ta Bada Umarnin Sake Zaben Fidda Gwani Na APC a Mazabar Sanatan Nasarawa Ta Yamma
- Babbar kotun tarayya da ke zamanta a Lafia ta yi hukuncin rushe zaben fidda gwanin APC na sanatan Nasarawa ta Yamma
- An shigar da APC kara tare da bayyana zargin yin magudi a zaben fidda gwanin da ta gudanar a watan Yuni
- Jam'iyyun siyasa a kasar nan na ci gaba da fuskantar rikicin cikin gida tun bayan kammala zaben fidda gwani
Lafia, jihar Nasarawa - Babban kotun tarayya da ke zama a birnin Lafia ta jihar Nasarawa ta rushe zaben fidda gwanin sanatan mazabar Nasarawa ta Yamma kana ta ba da umarnin a gaggauta sake yin sabo, Tribune Online ta ruwaito.
Mai shari'a Nehezina Afolabi ne ta bayyana hakan a hukuncin da ta yanke kan karar da Mr Labaran Magaji ya shigar kan kalubalantar jam'iyyar da wanda ya lashe zaben fidda gwanin.
A cewar mai shari'a, jerin sunayen deliget da suka kada kuri'a a zaben na ranar 4 ga watan Yunin 2022 na bogi ne, don ba Mr Shehu Tukur tikitin takara ya rushe bisa umarnin kotu.
Za a sake zaben fidda gwani cikin kwanaki 14
Ta kuma umarci jam'iyyar APC da ta gabatar da sabon zaben fidda gwanin sanata a mazabar cikin kwanaki 14 masu zuwa ta hanyar amfani da jerin sunayen deliget da INEC ta amince dashi.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Lauyan mai shigar da kara, Mr Ghali Ahmed ya ce za su duba shari'ar sannan su ba da martaninsu cikin sa'o'i 24 masu zuwa, Radio Nigeria ta tattaro.
A tattaunawa manema labarai suka yi da wanda ya shigar da karar, zai ci gaba da neman adalci domin cimma burin APC da kuma ilahirin masu kwarin gwiwa a kanta.
Idan baku manta ba, Magaji ya tunkari koru ne da zimmar ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zabe bayan da ya zargi magudi a zaben fidda gwanin da APC ta gudanar.
2023: Ku kwantar da hankali, za fa ku ci zaben nan, Buhari ga Tinubu da Shettima
A wani labarin, shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya yi batu mai ban dariya a fadarsa da ke Abuja yayin da yake martani ga zabo Sanata Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu na zaben 2023.
Shugaba Buhari, cikin barkwanci ya ba Tinubu da Shettima kwarin gwiwar lashe zaben shugaban kasa da ke tafe a shekara mai zuwa, Leadership ta ruwaito.
Buhari wanda ya karbi bakuncin dan takarar mataimakin shugaban kasa jim kadan bayan shugabannin APC da Asiwaju Bola Ahmed Tinubu sun kaddamar dashi, ya ce ya yi matukar farin ciki da zabo tsohon gwamnan na jihar Borno.
Asali: Legit.ng