Hadimin Mataimakin Gwamnan Jihar Kwara, Kayode Alabi, Ya Kwanta Dama

Hadimin Mataimakin Gwamnan Jihar Kwara, Kayode Alabi, Ya Kwanta Dama

  • Kehinde Obafemi, hadimin mataimakin gwamnan jihar Kwara, Kayode Alabi, ya riga mu gidan gaskiya ranar 30 ga watan Oktoba, 2022
  • A wata sanarwa da Sakataren watsa labarai na mataimakin gwamnan ya fitar, Alabi ya kaɗu da jin labarin rasuwar hadiminsa farat ɗaya
  • Kayode Alabi ya yi wa marigayin Addu'a kuma ya roki Allah ya ba iyalansa da abokanan arziki kwarin guiwar jure rashinsa

Kwara - Mataimakin gwamnan jihar Kwara, Kayode Alabi, ya yi rashin babban hadiminsa, Kehinde Obafemi, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.

Sakataren watsa labarai na mataimakin gwamnan, Modupe Joel, shi ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ranar Laraba, 1 ga watan Nuwamba, 2022.

Kehinde Obafemi da Kayode Alabi.
Hadimin Mataimakin Gwamnan Jihar Kwara, Kayode Alabi, Ya Kwanta Dama Hoto: channelstv
Asali: UGC

A cewar Sanarwan, mataimakin gwamna Alabi ya kaɗu da samun labarin rasuwar hadiminsa ba zato ba tsammani.

Kara karanta wannan

2023: Gaskiyar Abun da Ke Tsakanina Da Wike, Ortom da Sauran Jiga-Jigan PDP, Peter Obi Ya Fasa Kwai

Bayanai sun nuna cewa mamacin ya rasu ne ranar Lahadi, 30 ga watan Oktoba, 2022 bayan fama da gajeriyar rashin lafiya.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya yi Addu'a ga mamacin tare da miƙa ta'aziyya ga iyalansa.

Sanarwan tace:

"Mataimakin gwamna, Mista Kayode Alabi, ya ayyana mutuwar farat ɗaya ta shugaban hadimansa, Kehinde Obafemi, da wani abu da ya sa shi kaɗuwa ba tare da tsammani ba."
"Mista Kahinde Obafemi, ya rasu ne a ranar 30 ga watan Octoba, 2022 bayan fama da rashin lafiya ta kankanin lokaci. Har zuwa ƙarshen rayuwarsa ya kasance 'Chief Detail' ga mataimakin gwamnan jihar Kwara."

Alabi ya miƙa ta'aziyya ga iyalai

Mista Alabi ya yi Addu'ar Allah ya jikan mamacin tare da Fatan samu kwarin guiwar jure wannan rashin ga iyalansa da kuma abaokanan arziki.

"Mista Alabi ya yi addu'ar Allah ya jiƙan mariyagi Kehinde Obafemi kuma ya bai wa iyalansa, Abokanai da makusantansa kwarin guiwar jure wannan babban rashida suka yi," inji Sanarwan.

Kara karanta wannan

Abin da ya Haddasa Fadanmu da Murtala Garo a gidan Gawuna - Alhassan Doguwa

A wani labarin kuma Wani Mummunan Ibtila'i Ya Halaka Mata da Miji Da 'Ya'yansu Biyu a Birnin Kaduna

Wata mummunan Gobara ta yi ajalin mata da miji da 'ya'yansu biyu a jihar Kaduna ranar Lahadin da ta gabata.

Wani makocin mutanen ya bayyana cewa wutar da fara ne lokacin da 'yan NEPA suka dawo da wutar Lantarki da karfe 11:00 na dare.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Tags: