Siyasa: Jam'iyyar PDP tayi asarar tsohon sanata a jihar Taraba

Siyasa: Jam'iyyar PDP tayi asarar tsohon sanata a jihar Taraba

- Sanata Bashir Marafa ya mika takardar barin jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC

- A baya dai sanata Bashir Marafa ya rasa kujerarsa a kotu inda aka bawa sanata yusuf Abubakar

- Sanatan ya ce aikin Manbila Hydro-Power da shugaba buhari ya bayar da umarnin gudanarwa ya sanya shi komowa APC

Sanata Bashir Marafa, tsohon dan majalisar dattijai ya mika takardar barin babban jam’iyyar adawa ta PDP sannan ya mika takardar shiga jam’iyya mai mulki ta APC a hannun shugaban APC na riko a jihar.

Idan baku manta ba sanata Bashir Marafa ya rasa kujerarsa a kotu inda aka bawa sanata yusuf Abubakar kujerar bayan shari’ar da aka kwashe lokaci mai tsawo ana yi.

A lokacin da yake mika takardar komawa APC sanata Bashir ya yi alkawarin bawa jam,iyyar cikakkiyar gudummawa don ganin samun nasarar ta a dukkan zabukan dake gaba.

Siyasa: Jam,iyyar PDP tayi asarar tsohon sanata a jihar taraba
Sanata Bashir Marafa

Sanatan ya kara da cewa aikin Manbila Hydro-Power da shugaba buhari ya bayar da umarnin gudanarwa ne ya sanya shi komowa jam,iyyar ta APC, domin aiki ne da dukkan mutanen jihar suka dade suna fatan ganin anyi ta.

KU KARANTA: APC tana bin tsarin dokar siyasa Inji Gwamnan Osun Aregbosola

Idan dai baku manta ba a karshen makon nan ne Legit.ng ta ruwaito cewa tsohon mukaddashin gwamnan jihar Taraba, Alhaji Garba Umar, ya bayyana cewa ya yanke shawarar canza sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC bayan ya lura yadda zalunci ta yi yawa a jam'iyyar.

Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa Wannan: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng