Gobara Ta Yi Ajalin Miji da Mata da 'Ya'yansu Biyu a Jihar Kaduna

Gobara Ta Yi Ajalin Miji da Mata da 'Ya'yansu Biyu a Jihar Kaduna

  • Wata mummunan Gobara ta yi ajalin mata da miji da 'ya'yansu biyu a jihar Kaduna ranar Lahadin da ta gabata
  • Wani makocin mutanen ya bayyana cewa wutar da fara ne lokacin da 'yan NEPA suka dawo da wutar Lantarki da karfe 11:00 na dare
  • Magajin garin Maƙera, wanda ya tabbatar da faruwar lamarin ya yi wa mamatan Addu'a

Kaduna - Wasu Ma'aurata Mata da Miji da 'ya'yansu biyu sun rasa rayuwarsu a wata Gobara da ta tashi a Laying Dangan Waya dake yankin Rimaye a Rigasa, ƙaramar hukumar Igabi, jihar Kaduna.

Jaridar Daily Trust tace mummunan Ibtila'in ya auku ne ranar Lahadi da misalin ƙarfe 11:00 na dare lokacin da Ma'auratan Musa da Zaliha da kuma yaransu hudu ke cikin bacci a ɗaki.

Lamarin Gobara a Kaduna.
Gobara Ta Yi Ajalin Miji da Mata da 'Ya'yansu Biyu a Jihar Kaduna Hoto: dailytrust.com
Asali: UGC

Bayanai sun nuna cewa makotan gidan sun yi nasarar ceto biyu daga cikin 'ya'yan amma sun samu raunuka.

Kara karanta wannan

Bayan Mijinta Ya Gaza a Gado, Wata Mata Ta Faɗi Yadda Ya Gwada Kwazon Direbanta Har Ya Mata Ciki Sau 2

Wani maƙoci da ya bayyan sunansa da Sulaiman a taƙaice yace Gobarar da fara ne jim kaɗan bayan an dawo da wutar Lantarki, wacce mutane suka fi sani da NEPA.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Mutumin yace:

"Jim kaɗan bayan sun dawo da wuta na jiyo wata ƙara mai ƙarfi, na yi tunanin Turansufomar mu ce ta yi ƙara amma daga baya sai naga hayaƙi na tasowa daga ɗakin maƙotana."
"Mun yi ƙoƙarin kashe wutar amma bisa rashin sa'a ta riga da ta mamaye ɗakin baki ɗaya. Mun ci sa'ar ceto mutum biyu daga cikin yaran amma mahaifinsu, matarsa da wasu yaran biyu sun mutu a cikin wutar."

Magajin garin Makera, Malam Isiaku Abdulwahab Umar, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ayyana shi da babban abin takaici.

Basaraken ya yi wa Mamatan addu'an Rahama tare da fatan Allah ya baiwa ragowar yaran biyu lafiya cikin sauri.

Kara karanta wannan

Da Duminsa: Fashewar Janareto Ya Haddasa Mummunar Gobara a Legas

Legit.ng Hausa ta gano cewa tuni aka yi wa waɗanda suka rasu jana'iza kamar yadda Addinin Musulunci ya tanada.

A wani labarin kuma Fashewar Tukunyar Gas Ta Halaka Wata Matar Aure a Jihar Kwara

Fashewar tukunyar Gas ta halaka wata matar aure, Misis Adeola Adewale, a Egbe garage da ke yankin Omu-aran, ƙaramar hukumar Irepodun, jihar Kwara ranar Litinin.

Jaridar Leadership ta tattaro cewa lamarin ya auku ne da misalin ƙarfe 10:35 na dare lokacin da mamaciyar ke shirya wa iyalanta abincin dare.

Asali: Legit.ng

Online view pixel