Kaduna: El-Rufai Ya Kallafa Kudin Makaranta ga Daliban Sakandaren Jihar
- Gwamna Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna ya dawo da tsarin biyan kudin makaranta ga dukkan daliban dake manyan makarantun sakandare na jiharsa
- Kwamishinan ilimi ta jihar, Halima Lawal, ta sanar ta cewa kowanne dalibin da sauyin ya shafa zai dinga biyan N2000 a kowacce shekara daga tam mai zuwa
- Lawal ta sanar da cewa wannan matakin ya zama dole ne sakamakon rashin kayan aiki da kuma halin da tattalin arzikin kasar nan yake ciki yayin da yawan daliban ke cigaba da karuwa
Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta dawo da tsarin karbar kudin makaranta daga daliban manyan makarantun sakandare na jihar.
Kwamishinan ilimi ta jihar, Halima Lawal ta sanar da hakan a wata wasika da ta aikawa shugabannin makarantun sakandare na jihar a Kaduna.
Lawal tace sake dawo da tsarin karbar kudin makarantar an yi ne sakamakon rashin kayan aiki da jihar ke fama da shi, jaridar TheCable.ng ta rahoto.
Tace kowanne dalibi dake matakin babbar makarantar sakandare a jihar zai dinga biyan N2000 a kowacce shekara.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
“Karuwar yawan yaran dake makarantar gwamnati a jihar ne ya zama dole a kara fadadawa da gyara makarantun da ake da su, samar da kayayyakin koyarwa da na koyo domin samar da muhallin koyo mai inganci.”
- Kamfanin Dillancin Najeriya ya rahoto Lawal tana cewa.
“Sai dai rashin kayan aikin da jihar ke fama da shi sakamakon irin matsanancin hali da tattalin arziki ke ciki a wannan lokacin yasa aka sake dawo da biyan kudin makaranta a makarantun sakandare.
“Dalibai suna da zabin biyan kudin makarantar cikakke a farkon shekara ko kuma su biya kashi uku a kowanne tam na karatu.
“Dukkan shugabannin makarantun sakandare ana don su kiyaye cewa za a fara biyan kudin makarantar ne daga tam na biyu na zangon karatun 2022/2023.
“Za a aiko da tsarikan biyan kudin makarantar nan babu dadewa.”
Wannan cigaban na zuwa ne bayan shekaru da Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya ayyana ilimi kyauta ga dukkan dalibai mata a makarantun sakandare mallakin gwamnatin jihar a 2018.
Hakazalika, a shekarar 2020 Gwamnan ya umarci ayyana karatun firamare da na sakandare kyauta a dukkan fadin jihar.
Kaduna: El-Rufai ya ba da umarni ga makarantun gwamnati a koma karatun kwana 4
A wani labari na daban, Gwamnatin jihar Kaduna ta umurci dukkan makarantun gwamnati da su koma aikin kwanaki hudu a mako, yayin da za a bude makarantun a ranar 10 ga watan Janairu a zango na biyu na shekarar 2021/2022.
Kwamishiniyar Ilimi, Halima Lawal, ta ba da wannan umarni ne a Kaduna ranar Lahadi a cikin sanarwar dawowa karatu a zango na biyu na shekarar 2021/2022, Daily Nigerian ta rahoto.
Asali: Legit.ng