'Yan N500 da Aka Buga Shekaru 15 da Suka Gabata Sun Bayyana a Yayin da CBN Ke Shirin Sake Fasalin Kudi

'Yan N500 da Aka Buga Shekaru 15 da Suka Gabata Sun Bayyana a Yayin da CBN Ke Shirin Sake Fasalin Kudi

  • 'Yan Najeriya sun gano gudan N500 da aka buga shekaru 15 da suka gabata a daidai lokacin da CBN ke shirin sake fasalin Naira
  • A cewar jama'ar kafar sada zumunta, kudin da suka gani dole wasu 'yan handama ne suka adana tun shekarun baya
  • Babban bankin Najeriya ya ba da wa'adi zuwa 31 ga watan Janairu ga duk 'yan Najeriya kan su tabbatar sun rabu da tsoffin N200, N500 da N1000, za a kawo sabbi

Gabanin shirin gwamnatin Najeriya na sauya fasalin N200, N500 da N1000, 'yan Najeriyan da suka boye kudi sun fara ciro abin da suka boye.

A ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba, 'yan Najeriya suka fara gano sabbin 'yan N500 kal da aka buga tun shekarar 2007.

Kudaden da aka buga tun 2007 sun fara yawo a Najeriya
'Yan N500 da aka buga shekaru 15 da suka gabata sun bayyana a yayin da CBN ke shirin sake fasalin N200, N500 da N100 | Hoto: Westend61
Asali: Getty Images

Kudin da aka gani, babban bankin Najeriya ne ya buga shi tun 2007, shekaru shida kenan bayan kirkirar gudan N500 a Najeriya.

Kara karanta wannan

Rudani yayin da Gwamna El-Rufai ya yafewa wasu fursunoni hudu saboda wani dalili

Tsohuwa ajiya ta fara bayyana

A cewar wata wata 'yar Twitter, barakah_bello, kudin da aka gani dai akwai kamshin gaskiyar cewa, wasu 'yan handama ne suka adana, yanzu suka fitar saboda CBN ya jawo musu sabon liki.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ta ce:

"Ku duba fa shekaru 15 da buga N500 dinnan. Mutanen nan sun dade suna boye tattalin arzikinmu."

Sai kwatsam, wani ya yi martani da kalan kudin da ya samu tun na 2020 wanda aka ga sabo ne kal shima.

A kudin da aka gani, an ga sa hannun gwamnan CBN a wancan lokacin, wanda yanzu shine gwamnan jihar Anambra, Charles Chukwuma Soludo.

CBN ya sanar da yunkurin sauya fasalin wasu daga cikin manyan kudin Najeriya, tare da cewa wadanda suka boye kudin haram za su iya samun tsaiko wajen shigar da kudin banki.

Kara karanta wannan

CBN Zai Dagargaza Naira Tiriliyan 6 Cikin Shekaru 8 a Mulkin Shugaba Buhari

Hakazalika, CBN ya ce kudaden dake yawo a hannun jama'a sun yi yawa, ya kamata a samu mafitar yadda za su dawo banki, don haka ne ma za a kawo wannan sauyin fasali.

Kalli hotunan kudaden:

CBN Bata Ajiye Batun Gabatar da Gudan Naira 5,000 Ba, Inji Sanusi II

A wani labarin, tsohon gwamnan babban bankin Najeriya (CBN), Sanusi Lamido Sanusi ya bayyana cewa, gwamnatin kasar na kan bakanta na kirkirar gudan N5,000 a nan gaba.

Babban bankin Najeriya ya fara kawo batun yin gudan N5,000 a shekarar 2012, lokacin da Sanusi yake matsayin gwamna, lamarin da ya jawo cece-kuce a kasar, rahoton The Nation.

Masana tattalin arziki da dama a kasar sun yi ta tsokacin cewa, kawo gudan N5,000 zai dagula lamarin tattalin arzikin kasar, kuma zai kawo tsadar kayayyaki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.