Jagoran Kudu Mai Karfin Fada A Ji Ya Ragargaji Buhari Kan Karya Tsarin Mulkin Najeriya

Jagoran Kudu Mai Karfin Fada A Ji Ya Ragargaji Buhari Kan Karya Tsarin Mulkin Najeriya

  • Shugaban kungiyar Neja Delta, Edwin Clark, ya ce Shugaba Muhammadu Buhari ya karya doka saboda kin mika mulki ga mataimakinsa kafin ya yi tafiya
  • Clark ya ce duk wani mataki da mutanen shugaban kasar suka dauka ba halastacce bane yayin da ya ke kira ga yan Najeriya kada su lamunci saba dokar daga Buhari
  • Jagoran na Neja Delta ya kara da cewa Buhari ya jajantawa Korea ta Kudu da Indiya kan ifila'in da ya same su a kasashensu amma ya gaza ziyarar jihohi 20 da ambaliyar ruwa ta shafa a Najeriya

FCT, Abuja - Cif Edwin Clark, dattijon kasa daga yankin Neja Delta, ya ce Shugaba Buhari ya saba kundin tsarin Najeriya na 1999 saboda kin mika mulki ga mataimakinsa Yemi Osinbajo.

Clark ya yi wannan jawabin ne a ranar Talata, 1 ga watan Nuwamba, a taron manema labarai a Abuja, Channels Television ta rahoto.

Kara karanta wannan

2023: Atiku ya yi nadi mai muhimmanci, ya ba wani dan Katsina mukamin babban sakatare

Clark, Buhari
Jagoran Kudu-Maso-Kudu Mai Karfin Fada A Ji Ya Soki Buhari Kan Karya Tsarin Mulkin Najeriya
Asali: Facebook

A cewar shugaban na yankin Neja Delta, duk wani mataki da mutanen Buhari za su dauka a cikin makonni biyu ya saba wa doka.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Buhari da kundin tsarin mulkin Najeriya

Dattijon na kasa ya yi kira ga yan Najeriya kada su amince da duk wani abu da doka bata halasta ba.

Clerk ya yi zargin Buhari ya gaza samar da jagoranci mai kyau a Najeriya, don haka yana mamakin mai zai fita yi a kasashen waje.

Dattijon ya ce Buhari ya jajantawa Koriya ta Kudu da Indiya kan iftila'in da ya same shu amma bai iya ziyarar ko daya cikin jihohin Najeriya 20 da ambaliyar ruwa ya shafa ba duk da an rasa fiye da rayuka 600.

Babban Dattijon Neja-Delta ya fadi ‘Dan takara 1 daga Arewa da zai iya marawa baya a 2023

Kara karanta wannan

Ministan farko na sufurin jiragen sama a Najeriya, babban mai kare Nnamdi Kanu ya rasu

Babban ‘dan siyasar Kudu maso kudancin Najeriya, Edwin Kiagbodo Clark ya bada sharadin goyon bayan Bukola Saraki a takarar shugaban kasa.

Jaridar Daily Trust ta rahoto Cif Edwin Kiagbodo Clark ya fitar da wannan jawabi ne bayan ya hadu da ‘yan majalisar da ke taya Bukola Saraki yakin neman zabe.

Farfesa Iyorwuese Hagher wanda shi ne shugaban majalisar wayar da kan mutane game da takarar shugaban kasar Bukola Saraki ya zauna da Clark a Abuja.

Asali: Legit.ng

Online view pixel