Daruruwan Fusatattun Matasa Sun Rufe Babban Hanyar Bauchi-Tafawa Ɓalewa
- Wasu matasa da mutanen garin Yelwa Labura a jihar Bauchi sun tare hanyar Bauchi-Tafawa Balewa suna zanga-zanga
- Sunyi zanga-zangan ne kan zargin yan sanda sun saki wani Mohammed Damina, da ake zargin ya kashe mahaifin wata budurwa da ya ce yana so
- SP Ahmed Wakili, kakakin yan sandan jihar Bauchi ya ce wanda ake zargin har yanzu yana hannu kuma an tarwatsa matasan
Bauchi - Daruruwan matasa da mazauna garin Yelwa Labura a Bauchi, a ranar Litinin sun tare babban hanyar Bauchi-Tafawa Balewa don zanga-zanga kan sakin wani da ake zargi da kashe abokinsa, Adamu Babanta da matarsa.
Daily Trust ta tattaro cewa tun karfe 7 na safe, matasa sun taru a babban titin na Bauchi-Tafawa Balewa kusa da Kwalejin Noma, hakan ya janyo cinkoson ababen hawa na awanni.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Rundunar yan sanda ta yi karin haske kan abin da ya faru
Rundunar yan sandan jihar Bauchi ta tabbatar da afkuwar lamarin amma ta ce komai ya daidaita kuma an tura jami'ai wurin don tabbatar da zaman lafiya.
Kakakin yan sandan jihar, SP Ahmed Mohammed Wakili ya ce batun hatsarin mota da ya yi sanadin kisa daga Yelwa an tura zuwa MTD don bincike, "ana zargin kisa kuma wanda ake zargin, Mohammed Damina, yana tsare.'
Wakil ya ce:
"Wani mutum Mohammed Damina, Galadiman Dass, dan shekara 68 mazaunin Yelwa, ya nemi wata Khadijah Adamu Babanta da soyayya. Ta fada wa mahaifinta, kuma ta ce mutumin (Galadima) yana jiranta a gaban gidan man Total."
Kakakin yan sandan ya yi cigaba da cewa:
"Mahaifinta ya bi ta zuwa wurin, da isarsu, mahaifin, wanda yanzu ya rasu, ya fara yi wa mutumin magana ta gefen motarsa, a yayin da suke magana, Galadima ya fizgi motarsa yayin da marigayin ke makale a kofar motar har sai da ya fadi aka garzaya da shi ATBUTH a nan likita ya tabbatar ya rasu.
"Yau, Litinin misalin karfe 7 na safe, wasu bata gari sun taho titi suna zanga-zanga, suna tunanin an saki wanda ake zargin, amma ba a sake shi ba, yana tsare hannun yan sanda."
Bauchi: Raba Mata Da Maza A Makarantun Sakandare Ya Harzuka Dalibai, Sun Mamaye Tituna Suna Zanga-Zanga
A wani rahoton, daliban makarantun sakandare sunyi zanga-zanga a titunan Bauchi kan wata sabuwar doka da gwamnati ta kawo na raba mata da maza a makarantu.
Dalibai sun koma makaranta ne a hukumance yau (Litinin) a sassan jihar kamar yadda jaridar Vanguard ta rahoto.
Kwamishinan Ilimi na Jihar Bauchi, Mr Aliyu Tilde, ya ce gwamnatin jihar ta kammala shiri don raba dalibai mata da maza a makarantun jihar.
Asali: Legit.ng