Miyetti Allah Ta Nuna Ƙin Amincewa Da Gwanjon Miliyoyin Shanu Da Gwamna Ke Yi A Wata Babban Jihar Arewa

Miyetti Allah Ta Nuna Ƙin Amincewa Da Gwanjon Miliyoyin Shanu Da Gwamna Ke Yi A Wata Babban Jihar Arewa

  • Miyetti Allah ta yi tir da cigaba da kwace wa da gwanjon miliyoyin shanu da ake yi a jihar Benue
  • Kungiyar ta kuma nuna kin amincewarta da cigaba da tsangwamar fulani makiyaya da gwamnan jihar ke cigaba da yi
  • Shugabannin Miyetti Allah sun yi kira da cewa a kafa ma'aikatar gwamnatin tarayya na makiyaya

FCT, Abuja - Shugabannin kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah a jihar Benue sun nuna bacin rai da kin amincewa da kwacewa da sayar da miliyoyin shanu mallakar makiyaya a jihar.

Kungiyar kuma tana zanga-zanga kan cigaba da tsangwamar makiyaya fulani da gwamnan jihar ke cigaba da yi ta amfani da dokar hana kiwo a fili na jihar, The Nation ta rahoto.

Kara karanta wannan

El-Rufai ya tura malamai 2000 zuwa makarantu 155, zai inganta karatun mata a Kaduna

Miyetti Allah
Tashin Hankali Yayin Da Miyetti Allah Ke Zanga-Zangar Kin Amincewa Da Gwanjon Shanu A Benue. Hoto: Miyetti Allah.
Asali: Twitter

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugabannin kungiyar sun nuna bacin ransu a wani sakon bayan taro bayan zaman da shugabannin ta na jihohi suka yi a ranar Litinin 31 ga watan Agusta.

Shugaban kungiyar na kasa Abdullahi Bodejo da sakatarenta, Saleh Alhassan ne suka rattaba hannu kan sanarwar bayan taron.

Miyetti Allah ta nemi a kafa ma'aikata na musamman don makiyaya

Sun kuma yi kira ga gwamnatin tarayya, ba tare da bata lokaci ba ta ware tare da habaka filayen kiwo 415 a sassan kasar.

Kungiyar ta kuma yi kira ga gwamnati ta kafa ma'aikata na makiyaya da za ta rika ilimantar tare da magance kallubalen da makiyaya ke fuskanta.

Wani sashi na sanarwar ya ce:

"Taron ya yi Allah wadai da cigaba da tsangwamar makiyaya fulani da Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom ke yi, ta hanyar shedaniyar dokar hana kiwo da ya rika amfani da shi yana kwace miliyoyin shanu a iyakokin Benue-Nasarawa da Benue da Taraba."

Kara karanta wannan

Yanzu Yanzu: Shugaba Buhari Ya Jagoranci Taron Tsaro Na Gagggawa

Gwamna Ortom Ɗan Bindiga Ne, 'Yan Bangan Mu Za Su Kama Shi, Miyetti Allah

Kungiyar fulani makiyaya ta Miyetti Allah ta kira gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai da dan ta’adda, kuma ta lashi takobin kama shi matsawar EFCC ba ta damke shi ba.

Miyetti Allah ta zargi gwamna Ortom kwarai inda ta ce dan ta’adda ne shi. Ta kuma bayyana wannan zargin ne ta sakataren ta na kasa, Saleh Alhassan, ya yin tattauna wa da gidan jaridar Leadership.

Asali: Legit.ng

Online view pixel