Don Inganta Ilimin Yara Mata, Kaduna Ta Tura Malamai 2,000 Zuwa Makarantu 155 a Jihar
- Gwamnatin jihar Kaduna ta ayyana aniyarta na inganta karatun 'ya'ya mata a fadin al'ummomin jihar
- Mataimakiyar gwamnan jihar, Hadiza Balarabe ce ta bayyana zuba hannun jarin gwamnati ga fannin ba mata dama a jihar
- A cewar gwamnati, an tura malamai sama da 2000 zuwa makarantu sama da 150 a zagayen kananan hukumomi 23 na jihar
Duba da yadda ake yawan samun karuwar yara mata da ba sa zuwa makaranta a kasar nan, gwamnatin jihar Kaduna ta tura malamai 2000 zuwa makarantu 155 na fadin jihar.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, an tura malaman ne zuwa kananan hukumomi 23 na jihar domin ba da ilimi mai inganci.
Wannan na daya daga yunkurin gwamnatin EL-Rufai na tabbatar mai da yara zuwa makaranta tare da inganta ilimin 'ya'ya mata a cikin al'umma.
Mataimakiyar gwamna ta yi karin haske kan batun ilimin
Da take magana a wani bikin ilimin 'ya'ya mata na AGILE karkashin ma'aikatar ilimi na jihar, Hadiza ta ce shirin zai taimaka wajen habaka karuwar yara mata a makarantun jihar.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Hakazalika, ta ce shirin zai taimaka matuka wajen ba mata dama wajen baje-kolin baiwar da Allah ya yi musu, musamman a fannin ilimi.
Hakazalika, ta shaida cewa, gwamna El-Rufai ya ware kaso mai tsoka da ya kai 27% ga fannin ilimin domin tabbatar da an samu sauyi mai kyau a fannin.
A bangare guda, ta ce gwamnati na samar da kayayyakin aiki na zamani ga malamai domin tabbatar da an samu hanyoyin koyarwa masu sauki da tasiri a cikin al'umma, rahoton The Nation.
Gwamna El-Rufai Ya Yafewa Fursunoni Hudu Saboda Tuna Ranar ’Yancin Kai
A wani labarin, gwamna Mallam Nasir El-Rufai na jihar Kaduna ya yafewa wasu fursunoni hudu a bikin tunawa da ranar 'yancin kan Najeriya karo na 62 bisa ikon da kundin tsarin mulkin kasa ya bashi.
A cikin wata sanarwa da aka fitar daga gidan gwamna na Sir Kashim Ibrahim, an bayyana sunayen mutanen hudu da gwamna ya yafewa, rahoton TheCable.
Sun hada da Abdullahi Haruna, Usman Ahmed, Mohammed Sani da Khalillullahi Mohammed, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng