ACF Tayi Alkawarin Daukar Nauyin Karatun Daliban Jihar Kano

ACF Tayi Alkawarin Daukar Nauyin Karatun Daliban Jihar Kano

  • Kungiyar Arewa Consultative Forum reshen jihar Kano ta yi sabbin shugabanni kar kashi jagorancin Dr Faruk Gwani a zaben da tayi na wannan shekarar
  • Kungiyar ta sha alwashin fara biyan kudin makarantun gaba da sakandare ga daliban da suka gaza biyan kudin makaranta a jihar Kano
  • Kungiyar tace zata nemi ‘yan takarar gwamna a jam’iyyu daban-daban na jihar domin tabbatar da an samu cigaba a fannin ilimi, kiwon lafiya, noma da sauransu

Kano - Kungiyar Arewa Consultative Forum reshen jihar Kano tayi alkawarin kafa gidauniyar taimakon kudin makaranta ga ‘yan jihar da ba zasu iya biyan kudin karatunsu na makarantun gaba da sakandare.

Sabon shugaban kungiyar, Dakta zura Faruk Gwanin, ya bayyana hakan a Kano yayin jawabin amincewarsa inda yace wannan hukuncin ya zama dole saboda gwamnati na kasuwantar da fannin.

Kara karanta wannan

Shettima Ya Magantu Kan Tattaunawa da Kwankwaso Ya Koma Bayan Tinubu a Zaben 2023

Daily Trust ta rahoto cewa, sabbin shugabannin ACF an zabe ne babu abokan hamayya a taron shekara-shekara da suka yi a Kano.

Sabon shugaban ya kara da cewa, kungiyar zata nemi ‘yan takarar gwamnan daga jam’iyyun siyasa daban-daban kan tsarinta balle a fannin ilimi, kiwon lafiya, tsaro, nima da karfafa matasa da mata.

Kamar yadda yace, sabbin shugabannin zasu fifita fannin tsaro domin taimakawa hukumomin tsaro da kungiyoyin da kai wurin yaki da dukkan laifuka.

Yayin rantsar da sabbin shugabannin, shugaban kwamitin yardaddu na ACF ta Kano, Janar Halliru Akilu, yayi kra garesu da su tabbatar da amanar da aka basu.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Janar Akilu yayi kira ga sabbin shugabannin da su sanar da shirye-shirye da tsarikan da zasu kawo cigaban Kano da arewacin Najeriya.

Akilu, wanda ke daya daga cikin wadanda suka kafa ACF, yayi kira ga sabbin shugaban ina su hada kai da kungiyoyi irin su wurin kawo cigaba.

Kara karanta wannan

2023: Mutane Sun Fito Yayin da Ɗan Takarar AAC Ya Buɗe Kamfen Neman Gaje Buhari a Kano

Sauran sabbin shugabannin sun hada da Dr Muhammad Mustapha Yahaya wanda shi ne sakatare, Hajiya Aishatu Yakubu Maijama’a wacce ta kasance mataimakin Matar shugaban kungiya, Ambasada Dr Rufai Mukhtar Danmaje wanda shi ne mataimakin shugaba sai Farfesa Kamilu Sani Fagge matsayin mataimakin sakatare.

Sauran sun hada da Hajiya Rabi’aw Hussaini Adamu, Hajiya Mairo Bello, Alhaji Bello San Galadanci da Nasiru Yusuf Ibrahim.

2023: Abinda Ya Kamata 'Yan Najeriya Su Tambayi Kowane Mai Burin Gaje Buhari, Dattawan Arewa

A wani labari na daban, kungiyar dattawan arewa ta yi kira ga ‘yan Najeriya da su tambayi yan takarar shugaban kasa kan yadda zasu magance matsalolin kasar idan aka zabe su.

Kakakin kungiyar NEF, Hakeem Baba-Ahmed ne ya bayyana haka yayin da ya fito a shirin Sunday Politics na Channels TV.

Asali: Legit.ng

Online view pixel