Na Sayar Da Kadarorina Don Biyan Kudin Makarantar Daliban Jami'a, Kwankwaso
- Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana irin gwagwarmayar da yakeyi don daukan nauyin dalibai a jami'a
- Dan siyasan yace yanzu haka yana daukan nauyin dalibai sama da 1000 a jami'o'i masu zaman kansu a fadin Najeriya
- Tsohon gwamnan na jihar Kano yace a jiharsa ya dauki nauyin sama da dalibai 3000 lokacin yana mulki
Abuja - Dan takaran shugaban kasan jam'iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP), Rabi’u Kwankwaso, ya yi alkawarin cigaba da kokari don ciyar da Najeriya gaba.
Kwankwaso yace sai da ya sayar da kadarorinsa don cigaba da biyan kudaden makarantan daliban da yake daukan nauyi.
Kwakwaso ya bayyana hakan a taron lakcan murnar cikarsa shekaru 66 da gidauniyar Kwankwasiyya ta shirya a Abuja, rahoton PremiumTimes.
Tsohon gwamnan ya bayyana cewa Ilmi ne babban hannun jarin da dan siyasa zai baiwa mutane don inganta rayuwarsu.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Yace:
"Mun zabi dalibai 4 (Maza 2 mata 2) daga kowace jiha cikin jihohin Najeriya 36 da Abuja kuma muka dauki nauyinsu."
"Muna da sama da dalibai 300 a Jami'ar Igbinedion, sama da 200 a jami'ar Crescent da kuma 300 a jami'ar Bells. Gidauniyar tana daukan nauyin dalibai a ciki da wajen Kano."
"Akwai lokacin da na lura akwai wasu abubuwan da bana bukata, sai na sayar da dukkan wadannan abubuwa don wannan daukan nauyin na dalibai."
Buba Galadima: Kwankwaso Zai Kawo Dukkan Jihohin Arewa a 2023
A wani labarin, Buba Galadima, tsohon mamba a kwamitin yardaddu na jam’iyyar APC, yace Rabiu Kwankwaso ne zai lashe zabe a dukkan jihohin arewa a zaben shugabancin kasa na 2023 dake zuwa.
Kwankwaso shi ne ‘dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar NNPP mai alamar abarba, The Cable ta rahoto.
A yayin jawabi a ranar Alhamis a tattaunawarsa da Channels TV, Galadima yace Kwankwaso zai lashe zabe a shiyoyi uku na arewa kuma ya samu kuri’u a inda abokan hamayyarsa ke da karfi.
“PDP bata kan takardar kada kuri’a saboda karfi ta a kudu maso gabas ne wanda kuma Peter Obi suke yi. Wurin da PDP ke da karfi kuma shi ne kudu kudu. Kamar yadda Wike baya goyon bayan Atiku, kudu kudu ta kubuce masa.”
- Yace.
Asali: Legit.ng