Matashi Dan Najeriya Ya Nunawa Duniya Kyakkyawar Budurwarsa Farar Fata Tana Rangada Masa Girki a Bidiyo
- Wani matashi ya nunawa duniya kyakkyawar budurwarsa baturiya da yadda take kula dashi tamkar matarsa
- A wasu jerin hotuna da ya saki a soshiyal midiya, an gano budurwa tana girki kamar wata yar Afrika yayin da ta duka a gaban tukunyar gas
- Masu amfani da soshiyal midiya da dama sun nuna al’ajabi kan wannan nasara tasa inda suka nemi jin yadda aka yi ta fara soyayya da shi
Wani dan Najeriya mai suna @kanorsamuel223 a Tiktok ya wallafa wani bidiyo na baturiyar budurwarsa a dandalin.
A daya daga cikin hotunan an gano kyakkyawar budurwar tana amfani da tukunyar gas yar tsuguno don soya ayaba. Kuma ga dukkan alamu ta iya aikin gida sosai.
Matashi dan Najeriya da kyakkyawar budurwarsa
Ba don kalar fatar jikinta ba, mutum zai zata yar Najeriya ne duba ga yadda ta ke gudanar da harkokin girke-girkenta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Mutane da dama sun garzaya sashin sharhi na matashin don tambayarsa yadda aka yi ya samu wannan tsaleliyar budurwa a matsayin masoyiyarsa.
Kalli bidiyonsa a nan.
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin jama’a a kasa:
halo ya ce:
“Danuwa na samun nasara a rayuwa!!! yooooooooo!"
Dandy McCarthy:
“Tsafinka na da karfi sosai.”
Tik Toker ya ce:
“An samu katin dan kasa a turai.”
Your Stepdad ya ce:
“Abokiyar kasuwanci ta ki yarda ta koma faa.”
Matashi Ya Gwangwaje Matar Da Ke Bashi Abinci Kyauta Lokacin Da Bai Da Ko Kwabo, Ya Mallaka Mata Gida
A wani labarin, wata mai sana’ar siyar da abinci ta tsinci dami a kala inda ta mallaki gida nata na kanta bayan kyautatawar da ta yiwa wani matashi.
Matar wacce ke da kirki sosai ta dade tana baiwa matashin abinci kyauta sannan wasu lokutan ta siyar mai da abinci bashi.
Matashin ya fara shakku inda ya nemi jin dalilinta na kyautata masa, inda a karshe matar ta bude baki ta fadi dalilinta na aikata hakan.
Mai sana’ar abincin ta ce tana yi masa kallon mutum da zai yi nasara sosai nan gaba a rayuwa kuma tana son kasancewa cikin wadanda suka tallafa masa.
Ba a jima da yin haka ba, sai mutumin ya samu babban aiki sannan ya mallakawa matar da ke kyautata masa gida.
Asali: Legit.ng