Zargin Damfara: ‘Dan Takarar Sanatan APC a Kano Ya Ki Bayyana Gaban Kotu, EFCC
- Hukumar EFCC ta sanar da wata babbar kotun tarayya dake zama a Kano cewa AA Zaura yayi batan dabo, ya ki bayyana a gaban kotu har sau biyu
- Ana zargin ‘dan takarar kujerar sanatan APC a Kano ta tsakiya da damfarar wani ‘dan kasar Kuwait kudi har $1.3 miliyan, wanda a baya kotu ta wanke shi
- Sai dai lauyan wanda ake karan yace kotun bata da hurumin sauraron karar sannan wanda yake karewa bashi da lafiyar tsayawa a gaban kotun shiyasa bai bayyana ba
Kano - Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta sanar da babbar kotun tarayya dake Kano cewa Abdulkareem Abdulsalam Zaura wanda aka fi sani da AA Zaura, ‘dan takarar kujerar sanatan Kano ta tsakiya karkashin jam’iyyar APC yaki bayyana a kotu.
Ana zargin Zaura da damfarar wani ‘dan kasar Kuwait kudi har $1.3 miliyan kuma za a gurfanar da shi a ranar Litinin bayan kotun daukaka kara ta soke hukuncin da ya wanke shi tare da sallamarsa.
Sai dai, wanda ake zargin bai bayyana a kotun ba ranar Litinin kamar yadda bai yi ba a ranar 14 ga watan Oktoba da aka shirya fara shari’ar.
A yayin martani kan tambayar da alkali yayi mata, lauyan masu kara, Aisha Habib wacce ita ce shugabar bangaren shari’a na EFCC, tace wanda ake zargin ba a gan shi ba kuma rashin zuwansa kotu na nuna tsabar rashin mutunta kotun.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma lauyan Zaura, Ibrahim Waru, ya sanar da kotun cewa saboda sun shigar da wata bukata dake kalubalantar ikon kotun na sauraron shari’ar, wanda yake karewa ba dole ya kasance a kotu ba.
Ya kara da cewa, dalili na biyu shi ne, wanda yake karewa bashi da isassar lafiyar da zai tsaya gaban kotu kuma an samu bayanan likita.
Alkali Muhammad Nasiru Yunusa daga nan ya yi umarnin cewa lauyan wanda ake kara ya mika dalilan a rubuce a gaban kotun bayan samun sammaci saboda takardar asibitin a lokacin aka kawo ta.
Daga nan aka dage sauraron karar zuwa ranar 10 ga watan Nuwamba.
Daily Trust ta rahoto cewa, tun farko an gurfanar da AA Zaura a gaban alkali Lewis Allagoa na kotun kuma an sallame shi tare da wanke shi a watan Yunin 2020.
Rashin gamsuwa da hukuncin kotun yasa EFCC ta daukaka kara kuma aka kafa kwamitin alkalai uku a kotun daukaka karar karkashin jagorancin Abdullahi Bayero wanda yayi umarnin a sake shari’ar amma da wani alkali na daban.
Asali: Legit.ng