Wani Dan Najeriya Ya Fasa Asusun da Ya Yi, Ya Kirga Tsabar Kudi N5.5m a Cikin Wani Bidiyo
- Wani dan Najeriya ya jika zukatan jama'a a kafar TikTok yayin da ya fasa asusun da ya dade yana tara kudi a ciki
- Matashin mai suna Offwhite ya fara da cire wata katuwar akwati, ya fasa ta sai ga tarin kudi 'yan N1000
- Daga nan ya fara hada kansu, inda ya hada N500,000 a kowane dami tare da nuna wa mutane a wani bidiyo
Wani dan Najeriya ya shajja'a jama'a da dama a kafar TikTok yayin da cikin alfahari ya nuna kudin da ya tara a asusu da suka kai N5,000,000.
A wani bidiyon da ya yada a shafinsa mai suna @offwhite633, an ga lokacin da ya ciro katuwar akwatin da ya yi wannan asusu, kana ya fasa ta cikin tsanaki.
Mabiyansa a kafar TikTok sun shiga mamakin ganin yadda ya tara makudan kudade 'yan N1000 a cikin akwati kamar wannan.
N5,000,000 ya tara a asusu
Offwhite ya yada wani bidiyon bayan da ya gama fasa asusun tare da kirga abin daya tara a ciki. An ga damman N500,000 a ajiye a kusa dashi.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Da aka kirga yawan damman da ya tara, matashin ya hada N500,000 sau 11, kudin da suka kai kusan N5.5m kenan.
Bai dai bayyana yaushe ya fara tara wadannan kudade ba, amma alamu sun nuna ya dauki lokaci mai tsawo.
Kalli bidiyon:
Martanin jama'a
Mutane da dama sun yaba da irin wannan kokari da ya yi, kuma suka nuna sha'awar yin irin wannan ajiya na maganin watarana.
Wasu kuwa sun bayyana ba shi sha'awar ya gaggauta kai kudin ga banki kafin CBN ta aiwatar da batun sauya kudin kasar.
Ga kadan daga abin da mutane ke cewa:
@Chidera Dominic yace:
"Dan uwa ka kashe kudinka kafin su sauya kalar kudin kasar."
@juniorepelle yace:
"Nawa ne kudin mota Benz ne kam?"
@omejeobinna97 yace:
"Kai namiji ne, amma ba kowa ne zai gane ba. Na taya ka murna."
@Gina posh yace:
"Ya yi kyau tabbas kana da matukar kamewa wajen yin wannan. Na taba gwadawa, amma na gaza."
@wirelessbullet yace:
"Ka yi kokari gaskiya, ka dan sammin ka bani shawarin yadda zan yi ajiya haka ba tare da na fasa ba."
CBN da NMfB Sun Fara Bibiyar Asusun Wadanda Suka Ci Bashin Banki Na Lokacin Korona, Suna Cire Kudi
A wani labarin, Babban bankin Najeriya (CBN) da kuma bankin NIRSAL sun fara karbo kudaden da suka ba 'yan Najeriya rance a 'yan shekarun baya.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa, an fara karbo kudaden ne a ranar Juma'a 28 ga watan Oktoban 2022 ta hanyar amfani da lambar bankin bai daya na BVN.
Hakazalika, bankin na NIRSAL zai fara dawo da kudaden da 'yan Najeriya suka karba a lokacin Korona karkashin shirin TCF da kuma na 'yan kasuwa karkashin shirin AGSMEIS.
Asali: Legit.ng