Sojoji Sun Kashe `Yan Boko Haram 8 a Neja Bayan Wani Hari da Suka Kai a Barikin Soja
- Sojojin Najeriya sun yi nasarar fatattakar 'yan ta'addan Boko Haram da suka kai farmaki barikin soja a jihar Neja
- An hallaka 'yan ta'adda takwas tare da raunata da dama inji wasu majiyoyin da suka nemi a sakaya sunayensu
- Rundunar sojin Najeriya na ci gaba da samun nasara kan 'yan ta'adda a 'yan kwanakin nan, sun kashe da dama a Kaduna
Jihar Neja - Akalla 'yan ta'adda takwas aka hallaka da ake zargin 'yan Boko Haram ne a yankin New Bussa a karamar hukumar Borgu ta jihar Neja, inji rahoton Tribune Online.
Rahoton da muka samo ya bayyana cewa, wannan lamari ya faru ne a karshen mako bayan da 'yan ta'addan suka kai farmaki barikin soja a yankin don kubutar da 'yan uwansu dake tsare.
A cewar wasu rahotanni, an kuma kama wasu tsageru uku daga cikinsu, sai dai an ruwaito cewa, wasu daga jami'an sojojin sun samu raunuka a rikicinsu da 'yan ta'addan.
Yadda lamarin ya faru cikin dare
Wasu majiyoyi sun shaidawa jaridar Tribune Online cewa, 'yan ta'adda sun farmaki barikin sojan ne a daren Asabar da misalin karfe 12 na safe yayin da suka yi kokarin kutsawa don ceto 'yan uwansu dake tsare a ciki.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
An tattaro cewa, sojojin da suka yi daga da 'yan ta'addan sun nemi taimakon sojin sama, wadanda daga baya suka zo suka ci karfin 'yan ta'addan tare da fatattakarsu.
Don haka, rahotanni suka shaida cewa, wasu 'yan ta'adda da dama sun tsere da raunukan harbin bindigan da suka samu a kai ruwa rana da suka yi da sojoji.
Sojoji Najeriya Sun Kashe ’Yan Ta’adda da Dama a Jihar Kaduna
A wani labarin, rundunar sojin Najeriya na sashe na 1 da a jihar Kaduna sun share yankunan Maidaro, Kagi Hill, Kusharki da Anguwan Madaki a karamar hukumar Birnin Gwari daga 'yan ta'adda.
Wannan na fitowa ne daga wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar, birgediya janar Onyema Nwachukwu ya fitar, inda yace an kashe 'yan bindiga hudu kana wasu da dama sun tsere.
A bangare guda, an kwato bindigogi kirar AK-47 guda bakwai da kuma wasu bindigogi masu sarrafa kansu guda uku, AIT ta ruwaito.
Asali: Legit.ng