An Kama Wata Fatima Abubakar Da Ta Zuba Wa Mijinta Guba a Abinci Ya Mutu

An Kama Wata Fatima Abubakar Da Ta Zuba Wa Mijinta Guba a Abinci Ya Mutu

  • Yan sanda sun kama wata Fatima Abubakar bisa zargin yin ajalin mijinta ta hanyar amfani da guba a jihar Borno
  • Da aka zanta da Fatima, ta amsa laifinta kuma a bayananta tace ta tsani a aure ne baki ɗaya amma iyayenta kullum hakuri suka bata
  • Kwamishinan yan sandan Borno, Abdu Umar, yace tuni suka kamata kuma ana ci gaba da bincike

Borno - Hukumar yan sanda reshen jihar Borno ta kama wata matar aure, Fatima Abubakar, bisa zargin ajalin mijinta, Goni Abba ta hanyar amfani da guba, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kwamishinan yan sandan jihar, CP Abdu Umar ne ya bayyana haka ga hukumar dillancin labarai (NAN), yace dakarun Ofishin Anguwan Doki ne suka kama wacce ake zargin ranar 19 ga watan Oktoba.

Umar ya yi bayanin cewa lamarin ya auku ne lokacin da mutumin, babban limamin yankin ya dawo daga Masallaci, ita kuma Fatima watau matarsa ta biyu da zuba guba a abincinsa.

Kara karanta wannan

Katsina: ‘Yan Sanda Sun Yi Ram da Gagararren Dilallin Kwayoyi

Fatima Abubakar.
An Kama Wata Fatima Abubakar Da Ta Zuba Wa Mijinta Guba a Abinci Ya Mutu Hoto: dailynigerian
Asali: UGC

Kwamishinan yace nan take bayan Goni ya fara cin abincin lamari ya canza, aka yi gaggauwar kai shi Asibiti na musamman amma rai ya yi halinsa bayan sun koma gida.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Bayan samun rahoton abinda ya faru a Caji Ofis din GRA, nan take CP ya tura jami'an sashin bincike zuwa wurin domin cafke matar amma da zuwa suka taras matasa sun kewaye gidan zasu kasheta, Daily Nigerian ta rahoto.

Yace zuwan dakarun 'yan sanda suka dakile yunkurin matasan Anguwa da suka fusata kuma suka kama wacce ake zargin. Yace wacce ake zargin ta amsa laifinta kuma ta siyo gubar a Kasuwar Litinin.

Meyasa ta aikata wannan ɗanyen aiki?

Fatima, wacce aka nuna a Hedkwatar yan sanda, ta faɗa wa NAN cewa ta kashe mijinta ne sabida ta gaji da auren. Tace:

Kara karanta wannan

Hukumar EFCC Tayi Nasarar Daure 'Yan Damfara 2, 800 a Watanni 10 a 2022

"Bana son auren, Goni mijina ne na biyu, na rabu da na farko ne saboda na tsani aure. Duk lokacin da na wayi gari da tunanin ni matar aure ce, raina ɓaci yake, wani lokacin gida nake komawa na ce wa iyayena bana so amma su bani hakuri."
"Akwai wani lokaci, watanni biyu bayan na haihu, na gudu na bar gida na koma rayuwa a ƙasan wani kangon gini da ba'a ƙarisa ba tsawon mako biyu, daga baya na koma gidan mijina."
"Ba cutata yake ba kuma babu wani sabani tsakaninu, mu biyu ne matansa, ni ce ta biyu kuma mun yi aure tun 2021. Amma na tsani duk lokacin da namiji ya kusance ni."

Fatima Abubakar ta ƙara da cewa bata san abinda ke damunta ba, "Ko a yanzu da nake magana da ku bana ji a jikina na yi kisa," injita yayin da ta fashe da kuka.

Kara karanta wannan

Barazanar Tsaro: An Gano Asalin Dalilin Rudewa Amurkawa a Abuja

A wani labarin kuma Wata Mai Kudi a Abuja Na Neman Wanda Zai Dirka Mata Ciki, Zata Biya N3m kan wasu sharudda

Wata Mai kuɗi dake zaune a Birnin tarayya Abuja ta shiga neman kyakkyawan Saurayin da zai iya ɗirka mata ciki.

Attajirar ta yi alkawari baiwa duk wanda iya wannan aiki kuɗi naira Miliyan Uku amma akwai sharuddan da ta kafa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262