Mahara Sun Banka Wa Gidaje 10 Wuta A Wani Unguwa A Kano

Mahara Sun Banka Wa Gidaje 10 Wuta A Wani Unguwa A Kano

  • Wasu mahara sun kutsa unguwar Dan Jamfari da ke karamar hukumar Rogo sun kona gidaje a kalla 10 da raunata wasu
  • Mazauna garin sun tabbatar da cewa maharan sun afka musu ne cikin dare da adduna da sanda wai suna neman babur dinsu da aka sace
  • Hukumar bada agajin gaggawa na jihar Kano, SEMA ta ziyarci garin ta raba wa mutane kayan tallafi, ta kuma ce gwamnati na bincike

Kano - Mahara sun kutsa unguwar Dan Jamfari da ke kauyen Barbaji a karamar hukumar Rogo ta jihar Kano sun kona gidaje goma, rahoton Vanguard.

Babban sakataren hukumar bada agajin gaggawa na jihar Kano, Dr Saleh Jili, a ranar Juma'a ya ce hukumar ta jajantawa wadanda abin ya shafa kuma ta kai musu kayan tallafi.

Kara karanta wannan

Yadda Matashi Mai Shekaru 19 Ya Yi Garkuwa Da Kansa Ya Karɓi Fansar Naira Miliyan 1 Daga Mahaifinsa A Adamawa

Taswirar Jihar Kano
Mahara Sun Banka Wa Gidaje 10 Wuta A Wani Unguwa A Kano. Hoto: @MobilePunch.
Asali: UGC

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya ce gwamnati za ta yi bincike don gano maharan a kuma hukunta su.

Kayan tallafin da aka kai musu sun hada da buhunan simitin, kusoshi, buhunan shinkafa, buhanan masara da gishiri da fale-falen rufin gida.

An kuma basu tufafi, bokitai, man gyada da cokoli da dunkulen dandano.

Mazaunin garin ya bayyana yadda harin ya faru

Wani mazaunin garin, Malam Magaji Audu, ya ce maharan sun taho ne da adduna da sanduna.

Ya ce:

"Sun dara 200 suka shigo kauyen cikin dare suka rika zuwa gida-gida suna ikirarin cewa suna neman babur dinsu da aka sace.
"Maharan sun yi kokarin soka min wuka a gaban iyalai na kuma na ki fito musu da 'ya'ya na da suka yi ikirarin sun sace musu babura."

Audu ya yi bayanin cewa bayan kwana guda maharan sun dawo sun cinna wa gidansa da na wasu wuta, yayin da iyalansa suka tsere.

Kara karanta wannan

Jami'an DSS da NIA Sun Damke Yan Ta'addan ISWAP 35 A FCT Abuja

Hakimin Rogo ya tabbatar da harin

Alhaji Muhammad Maharazu, hakimin Rogo, ya tabbatar da harin ya kuma yaba wa hukumar SEMA bisa kayan tallafin da ta kawo wa mutanen.

Maharazu, wanda ya samu wakilacin sakatarensa, Bashir Tsoho, ya ce sarkin Karaye, Dr Ibrahim Abubakar II, ya bada dukkan tallafin da ya dace ga wadanda abin ya shafa ya kuma kai wa gwamnati rahoto.

Ba Sojojin Amurka Ne Suka Kai Samame A Abuja Ba, In Ji Mazaunin Unguwa

Sojojin Amurka ba su cikin wadanda suka kai samame a rukunin gidaje na Trademore da ke Lugbe, babban birnin tarayya, Abuja, in ji wani mazaunin unguwar, Daily Trust ta rahoto.

Mazaunin, wanda ya tabbatar an kawo samame unguwar, ya ce kawai dan kasar waje daya aka gani cikin jami'an da suka kawo samamen.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164