‘Yan Bindiga Sun yi Barna a Zamfara, Sun Dauke Mai gari, Sun Nemi a Biya Miliyoyi
- An kai hare-hare dabam-dabam a ‘yan awannin bayan nan a wasu garuruwan da ke jihar Zamfara
- A cikin wadanda suka fada hannun ‘yan bindiga har da Mai garin wani kauye mai suna Birnin Tsaba
- ‘Yan bindigan sun yi awon gaba da wani ma’aikaci da kuma dalibi da ke jami’ar tarayya da ke Gusau
Zamfara – Rahotanni sun ce ‘yan ta’adda sun yi awon gaba a Mai garin kauyen Birnin Tsaba a karamar hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara.
Wani mazaunin Birnin Tsaba, Mohammed Faruku ya shaidawa Punch cewa ‘yan bindigan sun dauke Mai garin da ‘danuwansa ne da asuba.
Da karfe 3:00 zuwa 4:00 na safe aka shiga gida, aka dauke wadannan mutane a kan babur. Abin da aka sani shi ne Sunan Mai Garin Alhaji Hashimu.
Wani ‘danuwan Basaraken ya shaidawa manema labarai a tsorace cewa wani gawurtaccen ‘dan bindiga a yankin ya dauki nauyin wannan ta’adi.
'Yan bindiga sun yi fushi
‘Yan bindigan sun sace mutanen ne a dalilin dauke masu sababbin babura biyu da jami’an tsaro suka yi. Sahara Reporters ta fitar da wannan rahoto.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Shi ma wani ‘danuwan wadanda aka dauke, Idris Abdullahi yace sun fara maganar biyan kudin fansa domin ganin an dawo da ‘yanuwan na su.
Da aka nemi jin ta bakin ‘yan sanda, ba a iya samun kakakin rundunar jihar Zamfara ta waya ba.
An dauke ma'aikacin jami'a
Premium Times ta kuma rahoto cewa baya ga Basaraken, an yi garkuwa da wani ma’aikacin jami’ar tarayya ta Gusau a babban birnin Zamfara.
Yanzu haka Kabir Rabiu wanda ma’aikacin sashen yada labarai ne a jami’ar yana hannun ‘yan bindigan a sakamakon wani hari dabam da aka kai.
A garin Gusau dinne kuma aka tafi da wani dalibi da aka bada sunan shi a matsayin Sulaiman Lawal
Aikin su Dan karami ne
Rahoton yace ana zargin yaran wani ‘dan bindiga da ake kira Dan Karami ne suka dauke Mai garin. Dan karami ya yi fice a yankin Zurmi da Jibia.
Wani mazaunin wannan kauye yace ‘yan bindigan su na neman N5m, sannan a fito masu da baburansu da jami’ai suka karbe a tsakiyar makon nan.
An dauke mutane a Legas
Kun ji rahotanni na zuwa cewa da alama an yi garkuwa da mutane a titin Legas-Ibadan, wannan lamarin ya auku ne cikin dare a ranar Juma'a.
Hakan na zuwa a lokacin da Kasashen ketare suka tabbatar da cewa akwai alamun za a kai hare-hare a garuruwan Najeriya, daga ciki har da Abuja.
Asali: Legit.ng