Mata Na Ba ’Yan Bindiga ’Ya’yansu Mata Saboda Kudi, Inji Kwamishinar Kaduna
- Kwamishina daga jihar Kaduna ta bayyana yadda 'yan bindiga ke mu'amala da mata a jihar ta Kaduna
- Ta bayyana cewa, wasu iyaye na tura 'ya'yansu mata ga 'yan bindiga domin kawai su samu kudin kashewa
- Ana ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro da hare-haren ta'addanci a jihohin Arewa maso Yammacin Najeriya
FCT, Abuja - Hafsat Baba, kwamishinar ayyukan jama'a ta jihar Kaduna ta bayyana cewa, yana da matukar muhimmanci a magance wasu matsaloli da suka dumfaro mata a jihar.
Ta bayyana cewa, akwai matan dake tura 'ya'yansu mata ga 'yan ta'adda saboda kawai su samu kudin kashewa, rahoton TheCable.
Hafsat ta bayyana hakan ne a ranar Laraba 26 ga watan Oktoba a tattaunawa ta 22 na majalisar kasa kan harkokin mata da ya gudana a Abuja.
Da take magana kan ci gaban diya mace da kuma tsaronta a makaranta, kwamishinar ta ce, iyaye mata dake tura 'ya'yansu aikace-aikace da tallace-tallace na taimakawa wajen kara yawan adadin yaran da ba sa zuwa makaranta.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A cewar alkaluman majalisar dinkin duniya sashen yara (UNICEF), kashi 60% na yara miliyan 10 da ba sa zuwa makaranta yara ne mata a Najeriya.
Mata na tura 'ya'yansu ga 'yan bindiga saboda kudi, inji kwamishinar Kaduna
Hakazalika, kwamishinar ta bayyana damuwa game da halayen wasu iyaye wajen tabbatar da tsaron 'ya'yansu a kasar nan, inji rahoton ICIR.
A cewarta:
"Mun yi magana game da rashin tsaro amma har yanzu akwai abin zargi kadan. Meye za a ce game da masu kai wa 'yan bindiga bayanai?
"Daga cikinmu suke, suna ba 'yan bindiga bayanai saboda sun mai da hakan kasuwanci. Na ga mata na ba da 'ya'yansu mata ga 'yan bindiga, su kwanta da 'yan bindiga domin kawai su sami kudi.
"Idan ka dubi titunanmu, za ka gansu suna yawo da roba a hannu kuma babban abin damuwa shine yanzu wadannan yaran su ne masu rike da iyalansu.
Amurka Ta Amince Da Ficewar 'Yan Kasarta da Ma'aikatan Ofishin Jakadancinta Daga Najeriya
A wani labarin, gwamnatin kasar Amurka ta amincewa 'yan kasar mazauna Najeriya da su fara fita daga kasar biyo bayan rahoton barazanar tsaro da hukumomin kasar suka samo, Channels Tv ta ruwaito.
A wani sakon ankararwa da kasar ta fitar a ranar Talata 25 ga watan Oktoba da yamma, ma'aikatar Amurka a Najeriya ta yi alkawarin ba da shawarwarin kariya da tsaron gaggawa ga 'yan kasar mazauna Najeriya.
Hakazalika, Amurka ta kuma shawarci 'yan kasarta dake Najeriya da su kasance masu boye kawunansu kuma su kasance a ababen zirga-zirgan kasuwanci idan suna son barin Najeriya.
Asali: Legit.ng