MURIC Ta Bukaci a Dauke Cibiyoyin JAMB, WAEC Daga Cocunan RCCG

MURIC Ta Bukaci a Dauke Cibiyoyin JAMB, WAEC Daga Cocunan RCCG

  • An sake samun rawar kafa tsakanin cocin RCCG da kungiyar kare hakkin musulmai ta MURIC kan wasu batutuwa
  • MURIC ta zargi cocin RCCG da tauye hakkin dalibai musulmai ta hanyar hana su shiga Redemption City domin rajistar jarrabawar JAMB da WAEC
  • Kungiyar ta MURIC ta nemi hukumomin jarrabawar guda biyu da su dauke cibiyoyinsu daga Redemption City domin ba musulmi hakkinsu

Kungiyar kare hakkin musulmai ta MURIC ta bukaci hukumomin jarrabawar WAEC da JAMB da su dauke cibiyoyinsu a cocin RCCG dake kan babbar hanyar Legas-Ibadan.

Kamar yadda yazo a rahoton Vanguard, daraktan MURIC, farfesa Ishaq Akintola ya bayyana bukatar dauke cibiyoyin ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba 26 ga watan Oktoba.

A sanarwar da ya fitar, Akintola ya zargi cocin RCCG da hana dalibai musulmai shiga Redemption City domin gudanar da hidimar jarrabawar WAEC da JAMB a harabarta.

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Manyan Kantunan Abuja Sun Fara Rufewa Sakamakon Labarin Cewa Za'a Kai Hari

MURIC ta nemi a hana WAEC a coci
MURIC ta bukaci a dauke cibiyoyin JAMB, WAEC daga cocunan RCCG | Hoto: guardian.ng
Asali: UGC

Ya bayyana cewa, an hana dalibai musulmai shiga harabar domin kai takardun shaidan biya na banki, duba sakamakon jarrabawa da dai sauran lamuran da suka shafi jarrabawa a cibiyoyin.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Ya kuma bayyana cewa, an sha kawowa kungiyar koke da suke da alaka da tozarta dalibai musulmai game da cibiyoyin jarrabawar dake cikin cocunan RCCG.

Batun da MURIC ta gabatar

A cewar sanarwar:

"Mun yi matukar kaduwa da muka gano cewa, cocin RCCG yana hana 'yan uwanmu musulmai shiga sansaninsa dake babban hanyar Legas-Ibdan domin yi harkar banki na duba WAEC, JAMB da sauran cibiyoyin jarrabawa.
"Me zai sa RCCG daukar matakin da ba za ta iya kare kanta ba? Masu gadi a bakin cocin RCCG sun hana musulmai shiga daidai da umarnin da manyan RCCG suka bayar. Meye duniya take komawa ne? Wurin ibada bai kamata ya baude daga kan gaskiya ba.

Kara karanta wannan

Yaki da badala: Jami'a a Kudu ta haramtawa dalibai shigar badala, sanya gajeren 'sikett' da yin 'tattoo'

"Sun kira hakan labarin karya. Meye amfanin kirkirar irin wannan zargi? Ba halinmu bane. Meye za mu samo daga kirkirar labari?"

Kungiyar Musulunci, MURIC, Ta Yi Martani Kan Haramta Saka 'Mini Skirt' A Makarantun Jihar Abia

A wani labarin, kungiyar musulunci ta MURIC ta yaba wa Gwamna Charles Soludo na Jihar Anambra kan haramta saka gajerun sket wato 'mini skirt' a makarantun mata na gwamnati da masu zaman kansu a jihar.

MURIC ta ce haramtawar ya yi daidai da neman yancin saka hijabi da kungiyoyin musulmi ke yi a Najeriya, Nigerian Tribune ta rahoto.

Kungiyar, cikin sanarwar da shugabanta, Farfesa Ishaq Akintola ya fitar ta ce matakin da Gwamna Soludo ya dauka kishin kasa ne da hangen nesa da ya dace sauran gwamnoni su yi koyi da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.