Bana Bukatar Matar Aure Tunda Na Iya Girki Da Goge-goge: Matashi Dan Shekaru 47 Ya Ki Aure
- Wani dan Najeriya wanda ya gaji dukiyar mahaifinsa kuma shima yana da arziki ya ki yin aure duk da dangi sun nusar da shi kan yin hakan
- A cewar wani danginsa, Timothy Obinna, mutumin ya ce tunda ya iya girki da tsaftar wuri, baya bukatar aure
- Yan Najeriya da dama sun yi martani kan wannan hukunci nasa inda wasu suka yi sha'awar fadin gaskiya irin nasa
Wani dan Najeriya mai suna Timothy Obinna, ya haddasa cece-kuce kan furucin da yayi game da dalilin da yasa maza masu kudi basa son yin aure.
Wallafar Obinna martani ne ga wata wallafa da @Makavelli275 yayi inda yake mamakin dalilin da zai sa mutum da ke karbar albashi (N65,577,000) duk shekara zai dunga gudun aure.

Asali: UGC
Ya bayyana cewa yana da wani kawu da zai cika shekaru 48 a 2023 kuma ya ki yin aure.
Duk da cewar mutumin na cikin kudi kuma ya gaji arzikin mahaifinsa, ya bayyana cewa baya bukatar mace a rayuwarsa saboda shi ya iya girki da gyara sosai.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da yake magana kan kawun nasa, Obinna ya kara da cewa:
“Amma ba zan yi karya ba gayen nan ya fi mahafiyata ma iya girki da gaske.”
Kalli wallafarsa a kasa:
Legit.ng ta tattaro wasu daga cikin martanin mutane:
@veraidoko3 ya ce:
“Ina ganin zai iya samun yara da kansa don su gaji dukiyarsa saboda haka babu bukatar ya ajiye mata. Aikin banza.”
@LivingstoneB5 ya tambaya:
“Kana nufin…kana jin dadin abuncinsa/girkinsa fiye da mahaifiyarka?
Obinna ya yi martani:
“Dan uwa dangi sun shawarci sau da dama kan ya bude gidan abinci nasa na kansa, a iya sanina ban taba cin abincin da ya fi nasa dadi ba.”

Kara karanta wannan
Ta Rabu Da shi Saboda Tayi Sabon Saurayi: Magidanci Ya Ruguza Gidajen Da Ya Ginawa Matarsa Da Surukarsa
@Akinwole_Fenwa ya ce:
“Na san wani haka nima. Mutumin nan ya iya girki, gyare-gyare da kula da bakinsa. Duk sanda aka taso masa da maganar aure. Sai ya ce: “babu sauran matan kirki a waje dan Allah, bana sowa kaina wahala.”
Kyakkyawar Budurwa Mai Shekaru 38 Ta Bazama Neman Miji A Intanet,Ta Fashe Da Kuka A Bidiyo
A wani labarin, wata kyakkyawar budurwa yar Najeriya mai suna Princess Mimi ta haddasa cece-kuce a soshiyal midiya bayan ta koka kan cewa har yanzu bata auru ba duk da yawan shekarunta.
Matashiyar mai shekaru 38 ta wallafa wani bidiyo a TikTok inda ta dungi sharban kuka a cikin wata mota yayin da take fallasa asirin zuciyarta.
Princess ta ce zata cika shekaru 39 a bana, kuma har yanzu bata yi aure ko mallakar da nata na kanta ba kuma bata da wani tsayayye da zai fito neman aurenta.

Kara karanta wannan
A kirga lafiya: Bidiyon mutumin da yazo siyan kaya da jaka cike da 'yan N10 ya tada kura
Asali: Legit.ng