Kotu Ta Jefa Matashin Kano Da Ya Saci Kudin Kakarsa N15m Kurkuku
- Bayan watanni shida a kotu, an jefa wasu cikin matasan da suka sace kudin wata mata a Kano
- Daya daga cikin matasan ne ya hada baki da abokansa wajen sace kudin Kakarsa kudi kimanin milyan 16
- An yanke masa hukunci ranar 6 ga wata yayinda aka yankewa dayan abokinsa hukunci jiya
Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta gurfanar da wasu matasa bakwai yan jihar Kano da Katsina gaban babban kotun jihar Kano.
Ana tuhumar matasan da laifin satan kudin wata mata wacce kakar daya daga cikinsu ne, Almustapha Nasir har N15m.
Alkali Nasiru Saminu a ranar Talata ya yankewa matasan hukunci a kotun dake zamanta a jihar Kano.
An kamasu da laifin sace N15m daga asusun bankin Kakar Almustapha Nasir.
Matasan sun hada da Badaru Munir (23); Aliyu Falalu ( 23); AlMustapha Nasir( 22); Haruna Salisu Abatua( 23); Ismail Salisu Jibia (22), Ishaq Aminu (19), an damke su ne a wurare daban daban tsakanin 6 da 7 ga watan Maris, 2022.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Tun ranar 6 ga watan nan kotu ta yankewa Almustapha Nasir saboda bayan gano shi ya sace SIM card din Kakar kuma ya kaiwa abokansa suka kwashe kudi daga asusunta.
Daya daga cikinsu Ishaq Aminu ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi yayinda aka karanto masa a kotu.
Saboda haka Lauya Salihu Sani ya bukaci kotu ta hukuntashi bisa doka.
Ita kuwa lauyarsa, Nuriyya Musa, ta roki Alkali ya tausayawa Aminu Ishaq wajen hukunci.
A hukuncin sa, Alkali Saminu ya jefa Ishaq kurkukun shekaru 3 da daman biyan tarar N100,000.
Ana Zargin Dan Gwamna Ganduje, Abba, Da Laifin Karkatar Da Dukiyar Gwamnati
A wani labarin kuwa, Jam'iyyar New Nigerian Peoples Party (NNPP) na zargin Abba Ganduje, dan gidan gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Ganduje da karkatar da wasu dukiyoyin jihar.
NNPP ta bukaci hukumomi su gaggauta bincikensa.
Abba Ganduje ne dan takarar kujeran majalisar wakilai na APC na mazabar Dawakin Tofa, Rimingado da Tofa.
Shugaban jam'iyyar ta NNPP, Umar Haruna Doguwa, ya bayyana hakan a jawabin da ya fitar.
Doguwa yace jam'iyyarsa ta gano yadda gwamnatin jihar ta karkatar da motocin hukumar amsan harajin jihar KIRS guda 30 wajen yakin neman zaben Abba.
Asali: Legit.ng