Kiwon Lafiya: Amfanin man kifi guda 10 a jikin dan Adam
Ana samun man kifi ne daga jikin kifaye ma su maiko kamar su trout, mackerel, tuna, sardines, herriing da salmon.
Akwai kusan kaso 30 na maiko a jikn kifaye, sai dai wannan kason yana banbanta ne daga kifi zuwa kifi.
Mai na kifi yana kunshe da sunadaran vitamin A da vitamin D wadanda suke da fa'ida mai yawa a jikin dan Adam.
Da yawa daga ikin masana kiwon lafiya ta fanni ci da sha wato NUTRITIONISTS suna shawartar mutane da su inga cin kifi mai yawa saboda irin amfanin da yake kunshe da shi.
KU KARANTA: Yadda miliyoyin mutane su ke fama da rashin abinci a Jamhuriyyar Kongo – UN
A wani bincike da aka gudanar shekaru 10 da suka gabata, ya bayyana fa'idaojin amfani da mai na kifi ke yi a jikin dan Adam. Ga su kamar haka:
1. Kariya daga cutar lakar cikin kashin baya
2. Cutar daji da take kama 'ya'yan maraina na maza
3. Cututtuka da suke kama uwa bayan ta haihu
4. Ciwon hauka
5. Kaifin basira a kananan yara
6. Ciwon zuciya
7. Kaifin gani na ido
8. Cutar kuturta
9. Cutar Mantuwa
10.Inganta lafiyar mai juna biyu da abinda ke cikinta
Don shawara ko bamu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku duba shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://business.facebook.com/pg/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng