Amurka Ta Amince Da Ficewar 'Yan Kasarta da Ma'aikatan Ofishin Jakadancinta Daga Najeriya

Amurka Ta Amince Da Ficewar 'Yan Kasarta da Ma'aikatan Ofishin Jakadancinta Daga Najeriya

  • Kasar Amurka ta amincewa wasu daga 'yan kasarta dake zaune a Najeriya da su fice bisa tsoron abin da zai biyo bayan nan kusa
  • Amurka da Burtaniya sun fitar da sanarwar cewa, akwai yiwuwar samun hare-hare a birnin tarayya Abuja
  • Gwamnatin Najeriya ta yi watsi da batun Amurka, ta ce Najeriya ta samu zaman lafiya tun bayan hawan Buhari a 2015

Gwamnatin kasar Amurka ta amincewa 'yan kasar mazauna Najeriya da su fara fita daga kasar biyo bayan rahoton barazanar tsaro da hukumomin kasar suka samo, Channels Tv ta ruwaito.

A wani sakon ankararwa da kasar ta fitar a ranar Talata 25 ga watan Oktoba da yamma, ma'aikatar Amurka a Najeriya ta yi alkawarin ba da shawarwarin kariya da tsaron gaggawa ga 'yan kasar mazauna Najeriya.

Amurka ta amince 'yan kasar su fara barin Najeriya
Amurka Ta Amince Da Ficewar 'Yan Kasarta da Ma'aikatan Ofishin Jakadancinta Daga Najeriya | Hoto: channelstv.com
Asali: UGC

Hakazalika, Amurka ta kuma shawarci 'yan kasarta dake Najeriya da su kasance masu boye kawunansu kuma su kasance a ababen zirga-zirgan kasuwanci idan suna son barin Najeriya.

Kara karanta wannan

Kuyi Watsi Da Maganar Amurka, Najeriya Tafi Zaman Lafiya Yanzu: Lai Mohammed

A bangare guda, ma'aikatar ta gargadi 'yan kasarta dake wajen Najeriya da su guji shiga kasar saboda barazanar tsaro da hare-haren da ake sa ran za su faru nan gaba kadan.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amurka da Burtaniya sun gargadi 'yan kasashensu game da zama a Najeriya

Idan baku manta ba, a ranar Lahadin da ta gabata ne gwamnatin Amurka da Burtaniya suka shawarci 'ya'yansu mazauna Najeriya da su kasance a ankare bisa rahoton barazanar tsaro da kasashen biyu suka samo.

Kasashen sun nuna akwai yiwuwar samun hare-hare a babban birnin tarayya Abuja, musamman a gine-ginen gwamnati, makarantu da sauran wurare da dama masu cikowa a birnin, rahoton Punch.

Sai dai, ministan yada labarai da al'adu a Najeriya, Alhaji Lai Muhammad ya yi watsi da wannan gargadi na kasashen Turai, tare da cewa Najeriya ta samu kwanciyar hankali tun bayan hawan Buhari a 2015.

Kara karanta wannan

Ta bayyana: Yan Boko Haram Suna Basaja Da Aikin Kanikanci, Tela da Kafinta a Abuja

Hukumar tsaron farin kasa ta DSS a Najeriya ta shawarci 'yan kasar da su kwantar hankula su ci gaba da harkokinsu, hukumomi na aiki don dakile duk wata barazanar tsaro.

Ba wannan ne karon farko da kasashen waje ke gargadin samun rahotannin tsaro ba.

Amurka da Burtaniya Sun Gargadi 'Ya'yansu Dake Najeriya Su Kula, Za a Iya Kai Hari Abuja

A wani labarin, gwamnatin Amurka da Burtaniya sun gargadi 'ya'yan kasashensu mazauna Najeriya da su kula, akwai yiwuwar samun hare-hare a Najeriya, musamman a babban birnin tarayya Abuja.

Wannan na fitowa ne daga sashen ba da shawari kan tsaro na ofishin jakadancin Amurka dake Najeriya, Premium Times ta ruwaito.

Ofishin ya kuma bayyana cewa, hare-haren ka iya aukuwa ne a gine-ginen gwamnati, wuraren ibada, makarantu, kasuwanni da shagunan siyayya, otal, mashawa, gidajen cin abinci da na wasanni har kan jami'an tsaro da sauransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.