Fitaccen Gwamnan Najeriya Ya Janye Harajin Da Ya Kakabawa Masu Talla, Masu Tura Baro Da Masu Faci A Jiharsa
- Farfesa Chukwuma Soludo, gwamnan jihar Anambra ya janye umurnin da ya bada na karbar haraji daga masu talla, masu amalanke da sauransu
- Soludo ya bayyana hakan ne a yayin da ya ke jawabi wurin taron haraji karo na biyu a gidan gwamnati da ke Awka
- Gwamnan ya bada umurnin cewa a tabbatar sanarwar ya isa ga wadanda abin ya shafa yana mai cewa bai kamata a rika karbar harajin hannun talakawa ba
Anambra - Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Charles Soludo, ya yi mi'ara koma baya ya soke dukkan harajin da ya saka wa masu tura amalanke, kanikawa, masu talla da sauran ma'aikata a jihar.
Gwamnan ya bada umurnin ne yayin jawabin da yi wa mutanen Anambra a taron hanyoyin samun haraji karo na biyu a gidan gwamnati a Awka, rahoton Daily Trust.
Yadda Dan Kwallon Najeriya Ya Nutse Bayan Ceto Fasinjojin 5 A Hatsarin Jirgin Ruwa Da Ya Ritsa Da Su
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar Soludo, masu talla, masu tura amalanke da baro, da kanikawa ba su cikin wadanda za su biya harajin a Jihar Anambra.
A dena karbar haraji daga wurin talakawa masu talla da faci da tura baro - Soludo
Gwamnan ya kara jadada cewa a tabbatar wannan sakon ya isa dukkan kasuwanin jihar Anambra.
Soludo ya ce:
"Masu tura amalanke ba za su biya wani kudi a jihar ba. Masu facin tayoyi a titi suma su dena biyan haraji ga kowa. Masu talla ma su dena biya. A dena matsa wa wannan talakawan.
"Wannan sakon ba na kungiyoyin kasuwanni bane. Idan aka samu hujjan ba su biya, za a soke kungiyar. Muna son gina al'umma inda za a karfafa marasa karfi kuma masu arziki za su iya samun karin kudin don samar da ayyuka da gina arziki."
Gwamnan Anambra Ya Bada Umurnin A Fara Yi Wa Masu Sana'ar Tura Baro Rajista A Jiharsa
Gwamnan Jihar Anambra, Farfesa Chukwuma Soludo, ya bada umurnin a fara yi wa masu tura baro, direbobin adaidaita sahu, direbobin bas da manyan motocci rajista a jihar.
An tattaro cewa ya dauki matakin ne domin inganta tsaro da kara samar da kuma tabbatar da suna biyan harajinsu a jihar, The Punch ta rahoto.
Sanarwar da sakataren dindindin na Ma'aikatar Sufuri ta Jihar Anambra, Mrs Louisa Ezeanya ta fitar, ya nuna cewa za a fara rajistan ne ta hanyar daukan hotuna da zanen yatsu.
Asali: Legit.ng