Harin Babban Asibiti a Neja: 'Yan Bindiga Sun Aike Da Sakon Bukatunsu
- Yan bindigar da suka yi awon gaba da mutane a babban asibitin Abdulsalam Abubakar da ke Gulu Jihar Neja sun gabatar da bukatarsu
- Masu garkuwa da mutane sun nemi a biya naira miliyan 90 kafin su sako sauran mutane 9 da ke a hannunsu
- Yan uwan wadanda abun ya ritsa da su sun dukufa neman yadda za su hada kudaden don gwamnati ta ce ba za ta biya ko asi ba
Niger - Tsagerun ‘yan bindiga da suka sace wasu ma’aikata a babban asibitin Abdulsalami Abubakar, Gulu da ke karamar hukumar Lapai ta jihar Neja sun bukaci a biya kudin fansa domin su sako sauran mutum 9 da ke hannunsu.
Daily Trust ta rahoto cewa masu garkuwa da mutanen sun nemi a biya naira miliyan 10-10 kan kowani mutum daya wanda jimlar kudin zai kama naira miliyan 90.
Maharan wadanda suka yi awon gaba da mutum 15 ciki harda ma’aikatan asibitin sun sako wata mata da wasu yara saboda ba za su iya tafiya zuwa inda suke son kaiwa ba.
Wata majiya da ta magantu game da tattaunawa da ke gudana ta ce yan uwan wadanda aka sace suna fafutukar ganin sun hada kudin domin su biya tunda gwamnati ta rigada ta ce ba za ta biya kudin fansa kowa ba.
DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar
Wata majiyar ta kuma ce:
“Yan uwan na bi gida-gida suna rokon tallafi.”
Wani ma’aikacin gwamnati wanda ya magantu kan sharadin sakaya sunansa ya ce yan uwan mutanen da abun ya ritsa da su suna fafutukar hada kudi don ganin an saki masoyansu domin gwamnati ba za ta biya yan bindiga fansa ba.
Ya ce:
“Yan bindiga sun bukaci naira miliyan 10 kan kowani mutum. Kuma manufar gwamnatin jihar shine cewa ba za ta biya masu garkuwa da mutane fans aba. Amma yan uwan suna kokarin hada kudin don su biya.”
Mazauna kauyen da dama sun tsere
A halin da ake ciki, manoma da daman a ci gaba da tserewa daga gidajensu zuwa cikin gari da birane da suka hada da Minna da Lapai, yayin da wasu suka koma zama da yan uwansu a Abuja da Suleja.
Hankula sun sake tashi ne bayan ajiye wata wasika da yan bindigar suka yi a ranar Laraba a kauyen Vulegbo, kilomita kadan daga garin Gulu, cewa za su kawo hari a ranar 30 ga watan Oktoba.
Legit.ng ta tuntubi wani mazaunin Lapai mai suna Mallam Usman don jin yadda abun yake a yanzu haka, inda yace gwamnati ta girke sojoji a garuruwan da abun ya faru.
Kan halin da ake ciki game da biya kudin fansar da maharani suka bukata, mallam Usman ya ce yanzu haka wasu sun fara siyar da gonaki da albarkatun gonarsu don biyan wannan kudi.
Ya ce:
“Gwamnati ta tura sojoji zuwa garuruwan a abun ya shafa. Yan haka ba za mu iya cewa ga lokacin da abubuwa za su daidaita ba saboda an kulle makarantu.
“Don hada kudin fansar da yan bindigar suka bukata wasu sun fara siyar da gonaki da albarkatun gonarsu. Hukumar agaji ma ta zo harma ta bayar da tallafin wasu yan kudade.”
“Yanzu haka gidanmu na nan cikin garin Lapai cike yake da yan uwanmu da suka fito daga chan Gulu. Muna sa ran Allah zai daidaita lamarin nan kusa.”
‘Yan Bindiga Sun Halaka Dan Sanda Da Wasu 22 Sannan Suka Kona Gidaje 50 A Wata Jahar Arewa
A wani labarin kuma, ‘Yan bindiga sun halaka mutum 23 ciki harda wani jami’in dan sanda sannan suka jikkata mutum 11 yayin da suka kai farmaki garin Gbeji da ke karamar hukumar Ukum ta jihar Benue.
Maharan sun kai mummunan harin ne a ranar Laraba, 19 ga watan Oktoba, jaridar Leadership ta rahoto.
Mai ba gwamnan jihar shawara ta musamman kan harkokin tsaro, Lt Col. Paul Hembah (rtd), wanda ya tabbatar da lamarin, ya ce dan sandan wanda ya ji mummunan rauni ya mutu ne a hanyar zuwa asibiti.
Yadda Dan Kwallon Najeriya Ya Nutse Bayan Ceto Fasinjojin 5 A Hatsarin Jirgin Ruwa Da Ya Ritsa Da Su
Asali: Legit.ng