Kaduna: Ana Zargin Dakarun NAF da Harbin ‘Da da Uba, Sun Karyawa Tsoho Cinya

Kaduna: Ana Zargin Dakarun NAF da Harbin ‘Da da Uba, Sun Karyawa Tsoho Cinya

  • Ana zargin sojojin saman Najeriya da bindige wani tsoho, karya masa cinya tare da harbin ‘dansa a yankin Barakallahu dake karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna
  • Kamar yadda ganau suka tabbatar, sojojin sun je rushe gidan tsohon mai suna Danjuma Adamu inda matasa da ‘dan mutumin suka yi yunkurin hana su rusau din
  • Sai dai ibtila’in ya fadawa Danjuma ne yayin da yaje tambayar me ke faruwa, sojojin sun buge shi tare da harbinsa kuma suka harbi ‘dan Jafet Danjuma

Kaduna- Ana zargin dakarun rundunar sojin dama da harbe wani mutum mai suna Danjuma Adamu tare da ‘dansa Jafet Danjuma kan hana rushe gidansu da suka yi a yankin Barakallahu dake karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.

Daily Trust ta gano cewa, wadanda aka harban suna asibitin Barau Dikko dake Kaduna inda suke samun kular likitoci.

Kara karanta wannan

Dakarun Sojin Najeriya Sun Dira Maboyar ‘Yan Bindiga Sun Halaka Masu Yawa a Kaduna

Daily Trust ta rahoto cewa, lamarin ya faru ne bayan wasu fusatattun matasa da mata sun rufe babbar hanyar Kaduna zuwa Zaria domin zanga-zanga, lamarin da ya bar matafiya a cikin cunkoso na tsawon awa daya.

Rahotannin da ba a tabbatar ba sun ce jami’an tsaron sun harbi waa mata wacce tazo tarwatsa masu zanga-zangar.

Daily Trust ta tattaro cewa, jami’an NAF da Operation Yaki sun je wurin da karfe 8 na safe yayin da masu gidaje a yankin suke coci inda suka rushe wani gida mai dakunan bacci biyu.

A lokacin da mai gidan ya dawo bayan makwabta sun sanar da shi abinda ke faruwa, ya tarar an rushe wani bangare na gidan.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kamar yadda ganau da ya bukaci a boye sunansa ya ce:

“A yayin da wani tsoho ya tambayi sojojin abinda ke faruwa, basu yi wa tsohon bayani ba kawai sai suka doka masa gindin bindigarsu.”

Kara karanta wannan

‘Yan Bindiga Sun Halaka Dan Sanda Da Wasu 22 Sannan Suka Kona Gidaje 50 A Wata Jahar Arewa

Majiyar ta kara da cewa:

“Basu kare lafiya da ‘dan mutumin ba, Jafet Danjuma tare da wasu matasan da suka tasowa sojojin a yunkurin hana su rushe gidan da cin zarafin babansu.
“Sai dai abun takaici yayin wannan ruguntsumi, sojojin sun harbe uban da ‘dansa kuma sun karya cinyar tsohon kuma yana asibitin kwararru na Barau Dikko.

A yayin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na NAF, Ibrahim Bukar, yace zai tabbatar sannan ya kira.

Zamfara: ‘Yan Sanda Sun Ceto Mutum 27 Daga Masu Garkuwa da Mutane

A wani labari na daban, rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta ceto mutum 27 da aka yi garkuwa dasu a kauyukan Akawa, Gwashi, Tungar Rogo da Anka wadanda ‘yan bindiga suka kai sansanoninsu na Gando/Bagega da dajikan Sunke a kananan hukumomin Bukkuyum da Anka a jihar.

Jaridar Punch ta rahoto cewa, a yayin jawabi ga manema labarai a ranar Asabar, kakakin rundunar ‘yan sandan, SP Mohammed Shehu, yace cetonsu ya biyo bayan rahoton da Rundunar ta samu ne kan cewa kungiyar ‘yan ta’addan sun kutsa wasu kauyuka a Anka da Bukkuyum inda suka sace mutane da ba a san yawansu ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel