Zaben 2023: Ministan Buhari Ya Shiga Tsaka Mai Wuya Bayan Zargin Da Ya Yi Wa Jonathan

Zaben 2023: Ministan Buhari Ya Shiga Tsaka Mai Wuya Bayan Zargin Da Ya Yi Wa Jonathan

  • Reno Omokri ya yi yunkurin karin haske kan gwamnatin tsohon mai gidansa, tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan
  • Omokri, a martanin da ya yi kan kalaman Festus Keyamo kan gwamnatin Jonathan, ya ce tsohon shugaban na Najeriya ya bar wa Shugaba Buhari daya daga tattalin arziki mafi saurin bunkasa
  • Omokri kuma ya yi wa Keyamo gargadi cewa ya rika mutunta mukaminsa na SAN kuma kada ya zubar da mutuncin mukamin da karerayi da maganganu marasa tushe

Festus Keyamo, SAN, ya sha ragargaza bayan ya yi wasu zarge-zarge kan gwamnatin tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan.

Keyamo, cikin wasu zarge-zargen, ya yi ikirarin cewa a shekarar 2015, Jonathan ya mika wa Shugaba Muhammadu Buhari tattalin arziki da ya kama hanyar nakasa.

GEJ da Buhari
2023: Ministan Buhari Na Shan Ragargaza Bayan Ya Yi Zargi Kan Jonathan. Hoto: (Buhari Sallau)
Asali: Twitter

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Kara karanta wannan

Goodluck Jonathan Ya Zama Dan Gudun Hijira, In Ji Gwamnan Bayelsa

Wani zargin da kakkakin kwamitin yakin neman zaben na Bola Tinubu ya yi cewa shine gwamnatin na Buhari ta tarar ana hako danyen man fetur ganga 700,000 ko 600,000 duk rana.

A martaninsa kan ikirarin, Reno Omokri, tsohon hadimin kafafen watsa labarai na Jonathan, ya yi kira ga Keyamo ya mutunta mukaminsa na SAN ya dena bata shi da karya.

A cewar Omokri, Keyamo yana da damar yi wa Tinubu kamfen ba tare da yin karya ga gwamnatin tsohon mai gidansa ba.

Kalamansa:

"Ina son in yi roko ga Festus Keyamo ya rika muntunta mukamin Senior Advocate of Nigeria da ya ke da shi kuma ya dena cin zarafinsa ta hanyar yin karya a bayyane. Zai iya yi wa Bola Tinubu kamfen ba tare da yi wa gwamnatin Jonathan karya ba."

Tattalin arzikin Najeriya karkashin gwamnatin GEJ

Da farko, don fayyace gaskiya, Omokri ya ce Jonathan ya mika wa Buhari tattalin arziki mafi saurin bunkasa na uku a duniya a cewar CNN Money, kuma mafi saurin bunkasa na hudu a cewa Bankin Duniya.

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: Tinubu ya yi magana mai girma game da bashin da ake bin Najeriya

Kudin da Najeriya ke da shi a asusun kasashen waje a lokacin Jonathan

Na biyu, Omokri ya ce Jonathan ya bar $2.07 a asusun rarar man fetur (ECA) da $3 biliyan a asusun kasashe masu cin gashin kansu a lokacin da ya mika wa Buhari mulki.

Omokri ya kara da cewa tsohon mai gidansa ya "bar wa gwamnatin mai shigowa $5.6 biliyan na rara isakar gas. Kuma, gwamnatin Jonathan ta bar $28.6 biliyan a asusun kasashen waje."

Danyen mai da ake hakowa a lokacin GEJ

Kazalika, a amsar da ya bawa Keyamo kan cewa gwamnati mai ci yanzu na hako ganga 700,000 ko 600,000 a kullum, Omokri ya yi martani da cewa a shekarar 2015 "gwamnatin Jonathan ta mika mulki ga gwamnatin Buhari lokacin ana hako ganga 1.9 biliyan duk rana."

Ya kara da cewa:

"A cewar Hukumar Kididdiga ta Najeriya, tsaka-tsakin adadin gangan danyen mai da ake hakowa kowanne rana a farkon wata uku na 2015 shine ganga miliyan 2.8 duk rana. Gwamnatin mu ne ta tarar ana hako 700,000 duk rana ta habaka shi zuwa kusan miliyan 2 duk rana.

Kara karanta wannan

Yanzu Haka: Buhari Ya Karrama Jonathan, Wike Da Wasu Mutum 42 Da Lambar Yabo

"Daga karshe, mun bar Naira kan N199 shine $1. Yau N750 ne $1. Mun bar bashin kasashen waje a $10.7 biliyan. Yau ya kusa $40 biliyan. Mun bar hauhawar farashin kaya a 9.6%. Yanzu yana N20.52%."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164