Yan Bindiga Sun Kai Wa Ayarin Motoccin Babban Malamin Addinin Nigeria Hari, Sun Kashe Mutum 7 Har Da Yan Sanda

Yan Bindiga Sun Kai Wa Ayarin Motoccin Babban Malamin Addinin Nigeria Hari, Sun Kashe Mutum 7 Har Da Yan Sanda

  • Wasu yan bindiga da ake zaton makasa ne sun afka wa ayarin motoccin Apostle Johnson Suleiman a kusa da Auchi, Jihar Edo bayan ya dawo daga Tanzania
  • Mutane bakwai sun mutu sakamakon harin cikinsu har da yan sanda uku masu tsaron babban malamin addinin na kirista
  • Mai magana da yawun yan sandan Jihar Edo ya ce ya samu labarin harin amma ba zai iya tabbatarwa ba sai ya ji daga bakin DPO na yankin

Jihar Edo - Yan bindiga sun kai wa ayarin motoccin Apostle Johnson Suleiman hari a kanyar Benin-Auchi, Jihar Edo, a ranar Juma'a sun kashe mutum bakwai ciki har da yan sanda uku.

The Punch ta tattaro cewa Suleiman ya dawo daga tafiya ne a kasar waje yana hanyarsa ta zuwa Jihar Edo inda yan bindigan suka kai masa hari a kusa da Auchi a jihar.

Kara karanta wannan

Yadda Yan Bindiga Suka Sace Mutum 13 Yayin Kazamin Harin Da Suka Kai Wani Kauye A Neja

suleiman
Yan Bindiga Sun Kai Wa Ayarin Motoccin Babban Malamin Addini A Najeriya Hari, Sun Kashe Yan Sanda. Hoto: @TheNationNews.
Asali: Twitter

Yayin harin, yan bindigan, an rahoto sun bude wa ayarin motoccin wuta, sun kashe yan sanda uku masu tsaronsa da wasu mutane hudu da ba a gano su wanene ba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Lauyan Suleiman, Samuel Amune, wanda ya tabbatarwa The Punch harin ya ce, faston ya dawo daga wani shiri ne da ya tafi a Tanzania, ya kuma sha da kyar.

Ya ce:

"Yana dawo daga tafiya ne ya kuma kai Auchi lokacin da wasu makasa suka afka masa. Yan sanda masu tsaronsa uku da wasu sun mutu. Ya yi tafiya kuma ya dawo kenan daga Tanzania inda ya halarci wani shiri a shekaran jiya.
"Yana hanyarsa ta komawa Auchi ne lokacin da yan bindigan suka kai masa hari kusa da Sabingida zuwa Warake, Auchi na da iyaka da Warake. Ya wuce Warake ya fara shiga Auchi harin ya faru."

Kara karanta wannan

An Yi Kazamin Arangama Tsakanin Yan Tasha Da Yan Kasuwa, Ana Fargabar Rasa Rayyuka

Wani kwararre a bangaren tsaro, Dickson Osajie, ya yi suka kan rashin tsaro a jihar, ya ce harin ya faru da rana tsaka.

Ya ce:

"Sun kai masa hari (Suleiman); mutum bakwai har da yan sanda sun mutu. Ba tsaro a kasar; mutanen mu suna yawo da bindiga a tituna ba a gane su ba. Abin damuwa ne."

Martanin yan sanda

Da aka tuntube shi, kakakin yan sandan Edo, Chuidi Nwabuzor ya ce:

"Ban dade da jin labarin ba; amma ba zan iya tabbatarwa ba. Bari in tuntubi DPO da ke kula da yankin."

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164