Yanzu Haka: Buhari Ya Karrama Jonathan, Wike Da Wasu Mutum 42 Da Lambar Yabo
- Shugaba Muhammadu Buhari ya bada sabbin lambobin yabo ga tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da wasu manyan Najeriya 43
- Wadanda suka samu lambar yabon na NEAPS sun hada da gwamnan Rivers, Nyesom Wike; Shugaban Majalisa, Ahmed Lawa da takwararsa na Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila
- Ana bada lambar yabon na NEAPS ne ga wasu zababbun yan Najeriya saboda gudunmawarsu da hidima ga al'ummar kasa
FCT, Abuja - Shugaba Muhammadu Buhari yana halartar wani taro don karrama tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan da wasu manyan yan Najeriya 43 da lambar yabo na ayyukan yi wa kasa hidima, NEAPS.
Ana gudanar da bikin ne a dakin taro na Conference room da ke fadar shugaban kasa a Abuja, The Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Cikin wadanda za a karrama akwai gwamnonin Najeriya 16, ciki har da Nyesom Wike na Jihar Rivers; Shugaban Majalisar Tarayya, Sanata Ahmad Lawan; Kakakin Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, da shugabannin hukumomin tsaro da aka karrama su da lambobin yabo daban-daban.
An kafa lambar yabon na inganci ne don karrama mutane da suka ciri tuta wurin yi wa Najeriya hidima, ko ta taimakawa dai-daikun mutane, jiha, gari ko kasa baki daya ta hanyar jagoranci mai inganci, ayyuka ko taimakon mutane.
Don samun lambar yabon, wanda za a bawa sai ya kasance ma'aikacin gwamnati ko mai zaman kansa wanda ke raye kuma ya dade yana kwazo a wani bangare na rayuwa, tare da halaye masu kyau kuma ya kasance kan gaba wurin yi wa al'umma hidima da kirkire-kirkire.
Dakaci karin bayani ...
Asali: Legit.ng