Ooni Na Ife Ya Sake Angwancewa Da Santaleliyar Budurwa A Karo Na 5, Ana Shirye-Shiryen Ta 6

Ooni Na Ife Ya Sake Angwancewa Da Santaleliyar Budurwa A Karo Na 5, Ana Shirye-Shiryen Ta 6

  • Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, ya sake angwancewa inda yan Najeriya ke ta cece-kuce game da auren nasa a na biyar
  • Basaraken ya angwance da Olori Aderonke Ademiluyi, wacce ita ce matarsa ta biyar, bayan ya auri ta hudu a cikin kasa da mako guda
  • Sabbin ma’auratan sun yi auren kasaita irin na gidan sarauta, kuma tuni bidiyoyin shagalin ya karade soshiyal midiya

Jama’a sun yamutsa gashin baki a soshiyal midiya yayin da Ooni na Ife, Oba Adeyeye Ogunwusi, ya angwance da mata ta biyar kwanaki biyar bayan auren mata ta hudu.

Basaraken ya auri Olori Aderonke Ademiluyi, a wani kasaitaccen biki da aka yi irin na sarauta a ranar Alhamis, 20 ga watan Oktoba, a fadarsa da ke Ile-Ife, jihar Osun.

Ooni na Ife da amaryarsa
Yanzu Aka Fara: Ooni Na Ife Ya Angwance Da Amaryarsa Ta 5, Ta 6 Na Hanya Hoto: @ooniadimulaife @citypeopletv
Asali: Instagram

Tuni bidiyoyin shagalin bikin basaraken kasar Yarbawan suka karade koina a shafukan soshiyal midiya.

Kara karanta wannan

Rashin Lafiya Ya Jawo Aka Gaggauta Fita da Atiku Kasar Waje - 'Dan Kwamitin Zaben APC

Aurensa da Gimbiya Aderonke na zuwa ne kwanaki biyar bayan ya auri matarsa ta hudu, Gimbiya Ashley Adegoke, a ranar 15 ga watan Oktoba.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Kamar yadda ya kasance a aure-aurensa na baya, ba a ga Ooni ba, maimakon haka ya samu wakilcin dogarai, bayi, manyan yan fada da ma’aikatan gidan sarauta.

Basaraken na kuma shirye-shiryen auren mata ta shida, Gimbiya Temitope Adesegun, a yan kwanaki masu zuwa.

Kalli bidiyoyin shagalin bikin a kasa:

Jama’a sun yi martani

Meerah_cul:

“A yanzu Ooni na Ife na daukar mata kamar yadda Messi ke jefa kwallaye a raga.”

_Deagram:

“Shi kadai ya san lokacin da zai dakata. Yanzu aka fara. Ta shida na hanya.”

Halys_hia:

“Shirin tallafawa mata.”

Ooni Na Ife Ya Sake Angwancewa Da Kyakkyawar Budurwa Karo Na 3 Cikin Makonni

A baya mun ji cewa jama’a na ta cece-kuce a shafukan soshiyal midiya kan aure-auren da Ooni na Ife, Oba Adeyeye Enitan Ogunwusi, ke yi a baya-bayan nan.

Kara karanta wannan

Wani Gwamna Ya Umurci Dalibai Da Ma’aikatan Gwamnatin Jiharsa Su Fara Sanya Kayan Gargajiya Ranar Juma’a

Yan makonni bayan ya auri matarsa ta biyu, attajira Mariam Ajibola Anako, babban basaraken kasar yarbawan ya sake auren mata ta uku mai suna, Tobi Phillips.

An gudanar da bikin auren wanda ya samu halartan makusanta a ranar Lahadi, 9 ga watan Oktoba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng