Yan Mata 2 Sun Lallasa Gardawa 4 Wajen Gasar Cin Malmalan Sakwara

Yan Mata 2 Sun Lallasa Gardawa 4 Wajen Gasar Cin Malmalan Sakwara

  • An yi gasar rige-rigen cin Dalar Sakwara a jihar Ekiti kuma Mata sun bada mamaki matuka
  • Duk da an fi su yawa, yan mata biyu sun kayar da dukka mazajen dake musharaka a gasar
  • Al'ummar Jihar Ekiti na alfahari da Sakwara kamar dai yadda Bahaushe ke alfahari da Tuwo

Wani bidiyon gasar cin sakwara ya bayyana a shafukan ra'ayi da sada zumunutar yanar gizo a makon nan.

Gasar da ta auku a jihar Ekiti, yankin Kudu Maso Yammaci Najeriya ya nuna cewa yan mata biyu suka kayar da gardawa hudu wajen rige-rigen cinye dalar Sakwara.

Yadda Bahaushe ke alfahari da Tuwon Masara, haka al'ummar jihar Ekiti ke alfahari da Sakwara.

Ekiti
Yan Mata 2 Sun Lallasa Gardawa 4 Wajen Gasar Cin Malmalan Sakwara Hoto: @ekititrends
Asali: Twitter

Cikin kasa da mintuna biyu, yarinyar farko ta tayar da dalar Sakwara har da lashe kwano.

Kara karanta wannan

Wasu Shugabannin PDP na Neman Tada Rikici, Sun ce An Ware Su a Yakin Zaben Atiku

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daga baya yarinyar ta biyu ta jijjige sakwaran ba tare da bata lokaci ba.

Jama'a a soshiyal Midiya sun yi Alla-wadai da wadannan samari da suka bari mata suka kada su a irin wannan gasa.

Kalli bidiyon na EkitiTrends ta daura:

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Tags:
Online view pixel