Shugabar Hukumar NIDCOM Ta Cire Rigar Mutunci, Ta Dirkawa Wani Zagi a Twitter
- Shugabar Nigerians In Diaspora Commission, (NiDCOM) ta rama zagin da wani ya yi mata a dandalin Twitter
- Babu gaira-babu dalili wani mutumi ya zagi Hon. Abike Dabiri-Erewa, yana kiranta ‘Mumu’ a gaban kowa
- Da Dabiri-Erewa ta maida masa martani, sai mutane suka ce bai kamata jami’ar gwamnatin ta biye masa ba
Abuja – Hon. Abike Dabiri-Erewa ta fito tayi magangamu a sakamakon harin da wasu Indiyawa suka kai wa mutanen Najeriya da ke karatu a kasar wajen.
A yunkurin haka, Sahara Reporters tace shugabar hukumar NiDCOM ta mutanen Najeriya da ke zaune a ketare, ta samu kanta tana zagin wani a shafinta.
Bayan ‘yar takaddama, sai Abike Dabiri-Erewa ta kira wani da “Ode” a shafinta na Twitter, ma’anar wannan kalma da harshen Yarbanci itace sakarai.
Wasu mutane da ke bibiyar Dabiri-Erewa a dandalin sada zumuntan sun yi tir da yadda ta biye masa, tayi zagi a fili a matsayinta na jami’ar gwamnati.
Gwamnati ta ceci 'Yan Najeriya a Indiya
Kafin abin ya faru, shugabar hukumar tarayyar tayi bayanin kokarin da gwamnatin Najeriya tayi na kare mutanen da ake kai wa hari a makarantun Indiya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da take bayani a ranar Litinin a shafinta, Dabiri-Erewa tace abubuwa sun dawo daidai a Jami’ar Gurgaon da ke kusa da birnin Delhi bayan sun sa baki.
Abin da ya jawo zage-zange a Twitter
Ana haka ne sai wani mutumi mai suna @sensegiver1 a Twitter, ya duro kan Dabiri-Erewa, har ya kira ta ‘Mumu’, wannan abin sam bai yi mata dadi ba.
“Ta tafi Indonesiya ta ga yadda ake wulakanta ‘Yan Najeriya. Mumun mata ta na goyon bayan gwamnatin da ta gaza. Tana cikin wadanda suka bada gudumuwar gazawar. Aikin banza!”
- @sensegiver1
A dalilin haka tsohuwar ‘yar majalisar wakilan ta maida masa martani, ta kira shi ‘Ode’.
"Ode! Ka tafi kasar Indonesiya ka dauko kwayoyi, kana shiga kungiyoyin asiri, sai ka zo kana rokon a cece ka daga hukuncin kisa.
Mun godewa Allah da hukumar NDLEA take ceton mutane irinku daga hukuncin kisa yanzu."
- Abike Dabiri-Erewa
Haba mana Abike Dabiri-Erewa!
Tribune tace hakan ya sa har tsohuwar Ministar ilmi, Madam Oby Ezekwesili tayi tir da wannan martani, ta bukaci Dabiri-Erewa ta goge abin da ta rubuta.
Amma tsohuwar ‘yar jaridar ta tsaya kan bakanta, tace babu laifi ta rama zagin da aka yi mata, don tana jami’ar gwamnati, ba za ta bari a wulakanta ba.
Rikici a jam'iyyar PDP
Dazu an ji labari Fasto Godfrey Gbuji yana ganin da zarar an yi waje da Sanata Iyorchia Ayu daga NWC, za a ga karshen rigingimun Jam'iyyar PDP.
Wani Gwamna Ya Umurci Dalibai Da Ma’aikatan Gwamnatin Jiharsa Su Fara Sanya Kayan Gargajiya Ranar Juma’a
Dama can kusoshin PDP irinsu Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike sun dage cewa dole a karbe shugabanci daga hannun Ayu domin daga Arewa ya fito.
Asali: Legit.ng