Hatta Mijina Yana Alfahari dani: Mahaifiyar Yara 2 Direban Tasi Ta Birge Jama’a a Bidiyo

Hatta Mijina Yana Alfahari dani: Mahaifiyar Yara 2 Direban Tasi Ta Birge Jama’a a Bidiyo

  • Wata matar aure ‘yar Najeriya ta bayyana sana’arta a bidiyo wanda hakan ya zaburar da jama’a masu yawa a Instagram
  • Kemi Toriola mai shekaru 35 a duniya ta zama direban tasi bayan da ta bar kasuwancinta sakamakon annobar COVID-19
  • Tace mijinta yana matukar alfahari da ita saboda ita da kanta ta siya motar kuma tana kai balans har ta zama mallakinta

Matar aure kuma mahaifiyar yara biyu wacce direban tasi ce wacce ta shawarci sauran mata da kada su saki jiki ba tare da neman na kansu ba.

Direban Tasi
Hatta Mijina Yana Alfahari dani: Mahaifiyar Yara 2 Direban Tasi Ta Birge Jama’a a Bidiyo
Asali: Original

Kemi Toriola wacce mahaifiyar yara biyu ce ta shiga sana’ar tukin tasi bayan annobar COVID-19 ya yi matukar illa ga kasuwancinta.

Kemi mai shekaru 35 tace tana da cikakken goyon bayan mijinta tunda shine ya taimaka mata ta samu mota wacce zata dinga biyan kudin a hankali har ta zama mallakinta.

Kara karanta wannan

Ke Tauraruwa Ce: Makauniyar ‘Yar Najeriya Ta Doke ‘Yan Mata 18, Ta Ci Gasar Kyau a Bidiyo

Kamar yadda Kemi tace, akwai matukar kyau idan mace tana da wani ‘dan abu da zata bai wa iyalanta gudunmawa a karshen kowanne wata.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Tace akwai kyau a baiwa namiji goyon baya kuma za a iya yin wannan ne idan ana yin wani aiki mai ma’ana.

A bidiyon tattaunawar da Legit.ng tayi da Kemi, an ganta da motarta yayin da ta shirya fita aiki.

Kalla bidiyon a kasa:

Soshiyal midiya sun yi martani

Jajjircewar Kemi ta janyo mata jinjina daga soshiyal midiya inda wasu suke kira ga sauran mata da su kwaikwayi jajircewarta.

Ga wasu daga cikin martanin:

@exclusively_prince yace:

“Na yaba mata kuma ta birge ni. Abun yabawa ne wannan kuma abunda ya dace a kwaikwaya.”

@afrokitchencookingchallenge tace:

“Mace tagari.”

@gimbiyafatimawaziri tace:

“Suna da samun kudi sosai.”

Bayan Auren Mata ta 3 a Makon da Ya Gabata, Ooni na Ife ya Auro Mata ta 4 a Makon nan

Kara karanta wannan

Da Duminsa: ASUU Ta Jaddada Cewa Har Yanzu FG Bata Biya Mata Bukatunta ba

A wani labari na daban, Ooni na Ile-Ife, Oba Enitan Oginwusi, Ojaja II ya auro sabuwar mata mai suna Ashley Adegoke inda ya shiga da ita fadarsa a cikin wani kasaitaccen biki.

Auren na zuwa ne bayan makonni da basaraken ya yi wani auren inda ya aura Mariam Anako a wani takaitaccen bikin.

An tattaro cewa, basaraken ya auri Adegoke a ranar Juma’a da ta gabata. Hakazalika an yi auren ne a gidansu amaryar dake titin Olubose kan titin Ede a Ile-Ife.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Khalid avatar

Aisha Khalid (Hausa editor) Aisha Khalid marubuciyar jaridar Legit.ng ce mai fatan shahara. Ta samu digirinta na farko a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria a shekarar 2018. Ta kwashe shekaru tana rubutu a fannonin siyasa, nishadi, tsegumi da sauransu. Za a iya tuntubar ta a adireshin email din ta kamar haka: aisha.khaleed@corp.legit.ng

iiq_pixel