BUA ya Sha Bam-bam da Dangote, Ya Aikawa Gwamnatin Kogi Takarda Kan Rikicin Fili

BUA ya Sha Bam-bam da Dangote, Ya Aikawa Gwamnatin Kogi Takarda Kan Rikicin Fili

  • Kamfanin BUA ya rubuta takarda bayan barazanar ‘yan majalisar dokokin Kogi na karbe wani fili
  • A wasikar da kamfanin ya aikawa gwamnatin jihar Kogi, ya nuna bai bukatar filin da aka taba ba shi
  • BUA ya koka cewa filin mai eka 50, 000 ba za iyi amfani ba saboda matsalar tsaro da rashin tituna

Kogi - Katafaren kamfanin nan na BUA, yace bai bukatar filin eka 50, 000 da gwamnatin jihar Kogi ta mallaka masa a wani lokaci a shekarar 2012.

Kamfanin ya aikawa Darekta Janar na hukumar da ke kula da filaye da cigaban birane takarda a kan batun filin, The Cable ta fitar da wannan rahoto.

Kamar yadda wasikar da kamfanin ya aika ta nuna, BUA bai taba karbar filin da aka ba shi ba wanda ‘yan majalisar Kogi ke neman ya biya kudin mallaka.

Kara karanta wannan

Kogi: Ana Tsaka da Rikici da Dangote, Yahaya Bello Yayi wa BUA Kiran Gaggawa

A cewar BUA Group, ba su iya amfana da kyautar filin ba saboda rashin abubuwan more rayuwa da ma kalubalen rashin tsaro a yankin da filin yake.

Ba mu amfana da filin nan ba - BUA

“Tun da Jihar ta gayyace mu a 2012 domin mu sa kudi a wannan fili, babu kokarin da gwamnatocin jihohi suka yi har yau domin nagance matsalolin tituna da za su taimaka wajen yin aikin da aka yi niyya.”

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

BUA Plc
Kamfanin BUA Hoto: www.thecable.ng
Asali: UGC

“A yanzu ba a iya kai wa ga filin sai ta ruwa kuma idan ba a kashe kudin da ake bukata, aka gina abubuwan more rayuwa ba, kasuwancin ba zai yiwu ba.
“Ana fama da tabarbarewar tsaro a yankin da kewayansa a shekarun bayan nan, wannan ya jawo babu wani mai hannun jari da zai iya fara wani aiki a yankin.”

Kara karanta wannan

Sanusi II ya fadi abin da ya kamata a yi don habaka kudin shigan man fetur a Najeriya

Kamfanin yace ya so ya yi aiki a jihar Kogi, kuma ya biya gwamnati duk kudin da ya kamata.

Wasikar tace kamfanin yana bin ka’idojin kasuwanci na adalci da gaskiya a duk inda yake neman kudi tare da garuruwa ko gwamnatoci da makamantansu.

Kamar yadda Daily Nigerian ta kawo rahoto, la’akari da wadannan dalilai ne kamfanin na BUA ya shaidawa gwamnatin Kogi cewa bai da bukatar filin.

“Lura da wadannan dalilai da muka bada, da matsalolin da ke tattare, muna neman sanar da ku ta wannan wasika ba mu bukatar cigaba da aikin da muka yi nufi.
Gwamnatin Kogi za ta iya karbe filin idan ta ga dama."

Dukiyar Kanawa a Najeriya

Kwanaki kun ji labari Abdulsamad Rabiu shi ne mutum na biyu a jerin Attajiran da suka fito daga jihar Kano, maganar da ake yi, yana da Dala biliyan 3.2.

Shugaban kamfanin na BUA, mutum ne mai son yin kyauta kwarai da gaske.

Kara karanta wannan

Manta da Elon Musk, Ga Labarin Mansa Musa, Basaraken Afrika da ya Ninka Musk Arziki

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng