Gwamna Zulum Ya Ba da Umarnin a Fara Koyawa Almajirai Sana’o’in Hannu a Borno

Gwamna Zulum Ya Ba da Umarnin a Fara Koyawa Almajirai Sana’o’in Hannu a Borno

  • Gwamnan jihar Borno ya ba da umarnin a gwama karatun sana'a da na allo a Tsangayoyin jiharsa dake Arewa maso Gabas
  • Rahoton da aka ba gwamnan ya nuna adadin dalibai, malamai da makarantun allo da Islamiyya da ake dasu a jihar
  • Jihar Borno na daya daga cikin jihohin da suka sha fama da matsalar Boko Haram, har yanzu ana ci gaba da tasirantuwa da barnar 'yan ta'adda

Jihar Borno - Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya ba da umarnin a gwama fannin koyarda sana'o'i da Tsangayoyin almajirai 2,775 da makarantun Islamiyya 451 a fadin jihara.

Gwamnan ya ba da wannan umarnin ne a gidan gwamnatin jihar yayin da yake karbar bayanai game da tantance Tsangayoyi da makarantun Islamiyya a karkashin majalisar gwamnati ta makaratun Islamiyya da Tsangayu ta jihar.

Kara karanta wannan

Kamfen 2023: Ba a yi nisa ba, INEC ta fara kuka da yadda jam'iyyun siyasa ke kare jini biri jini

Gwamna Zulum ya ba da umarnin a fara koyar da sana'a a makarantun allo da Islamiyya
Gwamna Zulum Ya Ba da Umarnin a Fara Koyawa Almajirai Sana’o’in Hannu a Borno | Hoto: @GovBorno
Asali: Twitter

Wannan batu na Zulum na kunshe ne a cikin wata sanarwa da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Talata 18 ga watan Oktoba.

Manufar Zulum na kawo shirin sana'a a Tsangaya

Gwamnan ya bayyana cewa, shirinsa na gwama sana'o'i a makarantun allo da na da Boko wani yunkuri ne na ba daliban Tsangaya damar shiga jami'a da cibiyoyin ilimin gaba da sakandare.

DUBA: Bibiyemu a Instagram don samun labarai masu muhimmanci kai tsaye cikin manhajar

Ya kuma bayyana cewa, koyar da sana'o'in zai rage yawan adadin yaran da ba sa zuwa makaranta a fadin jihar.

Hakazalika, hakan zai rage yawon bara na almajirai dake karade tituna da lunguna har ma da sako a fadin jiharsa.

Da yake magana, shugaban majalisar gwamnati ta makaratun Islamiyya da Tsangayu ta jihar, Khalifa Ahmad Abulfatahi, ya gabatar da sakamakon bincike da tattara Tsangaya a zagayen kananan hukumomi 27 na Borno.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: Gwamnatin Buhari ta gani makarantun bogi 349 a jihar Arewa dake cinye kudin ciyar da dalibai

Sai dai, ya ce, binciken majalisar bai ga nasarar kaiwa ga kananan hukumomin Kala-Balge, Guzamala da Abadam na jihar.

Ya bayyana cewa, majalisar na da makarantun Tsangaya 2,775 tare da malamai 12,309 da kuma dalibai 224,068.

A cewarsa, akwai dalibai 128,789 dake karatun jeka-ka-dawo da kuma 97,279 dake karatu a makarantun kwana.

Majalisar ta kuma gani makarantun Islamiyya 451 dake aiki a fadin jihar.

Asali: Legit.ng

Online view pixel