Bidiyon Beran da Ya Shiga Dakin Ajiye Tabar Wiwi a Ofishin NDLEA Ya Ba da Mamaki
- Hukumar NDLEA ta yada wani bidiyon lokacin da wani bera ya yi batan hanya ya fada dakin ajiye miyagun kwayoyi
- An ga beran ya hauragiya a cikin ofishin, lamarin da ya ba mutane da dama mamakin ganin bakon abu
- Bayan da wata jarida sake yada bidiyon, mutane da dama sun yi martani mai zafi, sun fadi ra'ayoyinsu
Najeriya - Wani bera ya yi batan hanya, ya fada wurin da bai kamata ya tsinci kansa ba a ofishin hukumar yaki da hana shan miyagun kwayoyi ta NDLEA.
Hukumar ta yada bidiyo na yadda beran ke fagauniya bayan shakar kayan shaye-shaye da hukumar ke kwatowa a kai ma'ajiyar hukumar.
Bidiyon da mai magana da yawun hukumar, Femi Babafemi ya fitar a ranar Litinin a shafinsa na LinkedIn ya nuna irin dabi'un da beran ke yi da ba a saba gani ba.
Alamu sun nuna wannan beran dai na wasu gane-gane ne marasa ma'ana, don haka yake bibiyar wutsiyarsa tare da tsalle da mikewa cikin kaduwa.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
Da yake yada bidiyon, Babafemi ya ce:
"Wannan beran a ranar Juma'a cikin rudu ya shiga dakin ajiye kayan maye, inda aka ajiye tabar wiwi da daya daga ofisoshin NDLEA kuma bayan mintuna kadan, sai ya fara burburwa."
Daga nan ya shawarci mutane da su guji ta'ammuli da miyagun kwayoyi tare da bayyana gargadin suna da illa ga lafiyar jiki da ta dabi'a.
Kalli bidiyon:
Jama'a da dama sun yi martani
Jim kadan bayan da jaridar Punch ta yada bidiyon a Twitter, mutane suka fara bayyana ra'ayoyinsu game da beran. Ga dai abin da suke cewa:
@sunday_morayo
"Ya ci fiye da yadda zai iya taunawa."
@Juice_submit
"Babu mamaki, shi yasa NDLEA ke kone shaida."
@hoodkeed
"Ta yaya hakan zai warware matsalar Najeriya?
@dele_ogunji
"Wannan zai zama abin wayar da kan jama'a da kuma murmurewar wadanda tuni dama sun yi nisa Amma, tabbas, mutane za su ke cewa hakan ba zai faru dani ba."
@imiegha_moses
"Suna dana tarko ne tare da shirin cewa 'yan Najeriya bera sun cinye hodar iblis din da suka ajiye a matsayin kayan laifi."
'Yan Sanda Sun Dura Kan Gungun 'Yan Fashin Da Suka Yi Mummunan Barna a Abuja
A wani labarin, rundunar 'yan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta dura kan wani gungun 'yan ta'addan da ake zargin su suka yi fashi a wani shagon magani dake yankin Maitama a birnin tare da sace wata mota 'Prado'.
A baya rahoto ya bayyana yadda 'yan ta'adda suka zo da makamai tare da yin mummunan fashi a shagon maganin hadi da kashe wani mutum da ya yi kokarin kawo musu tsaiko a yunkurinsu na sace mutane.
A ranar Alhamis 13 ga watan Oktoba, kwamishinan 'yan sandan FCT, Sunday Babaji ya gabatar da wani da ake zargin yana daga cikin wadanda suka aikata barnar, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng