Ga Arzikin Man Fetur, Amma Babu Kudin Shiga, Sanusi II Ya Koka Kan Kudin Shigan Najeriya
- Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya bayyana alhininsa game da yadda kudin shigan man fetur ke tafiya a Najeriya
- Sanusi ya ba da shawarin raba NNPC tare da cire tallafin mai idan ana so kasar ta dogara da kanta da kudin shigan mai
- An yi taron zuba hannun jari na 7 a birnin Kaduna, an gayyaci baki, tsohon sarkin Kano na daga cikin wadanda suka halarta
Kaduna - Tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II ya siffanta Najeriya a matsayin kasar dake da arzikin man fetur amma babu kudin shiga, inda ya bayyana kaduwa da halin da tattalin arzikin kasar ke ciki.
Sanusi ya bayyana hakan ne a karshen makon jiya a yayin taron zuba hannun jari karo na 7 da aka gudanar a jihar Kaduna, rahoton TheCable.
Hakazalika, tsohon gwamnan na babban bankin Najeriya (CBN) ya kadu da yadda kudin shigan man fetur ke yin kasa a cikin shekaru 10 da suka gabata.
A cewarsa:
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
"Baya ga kalubale a matakin duniya, Najeriya na da nata matsaloli na karan kanta.
"Kudin shigan mai, wanda a da shine madogarar gwamnatin tarayya, na ta yin kasa a cikin shekaru goma. Wannan na faruwa ba tare da la'akari da muhallin farashin mai ba."
A cire tallafi, a raba NNPC, inji Sanusi
Hakazalika, ya fadi hasashen kudaden shiga na gwamnatin tarayya a shekarar nan, duk da haka, ya ce a kullum gwamnati na tsara abin da take son samu, amma sam hakan ba ya tabbata a kowacce shekara.
A bangare guda, Sanusi ya ce babbar matsalar Najeriya itace kudin tallafin mai da gwamnati ke sanyawa, kuma hakan na kawo cin hanci da rashawa ga kudin shigan daga man fetur a Najeriya.
Daga karshe ya ba da shawarin raba kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC) tare da cewa kamfanin ne matattarar duk wata badalaka, inji rahoton Punch.
Kasafin Kudin 2023: 1.35 Tiriliyan Za a Ware Don Yaki da Boko Haram da ‘Yan Bindiga
A wani labarin, a yayin da ake cigaba da yaki da matsalar tsaro, gwamnatin tarayya ta ware N1.35 tiriliyan domin cigaba da yaki da rashin tsaron da ya addabi kasar nan.
Wannan na kunshe ne a kasafin kudi N20.51 tiriliyan na 2023 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gabatarwa majalisar tarayyar kasar nan a ranar Juma’a.
Binciken da Punch tayi ya nuna cewa, daga cikin N1.35 tiriliyan din da ake son warewa, ma’aikatar tsaro da sojoji za a ware musu N1.28 tiriliyan domin yakar Boko Haram, ‘yan bindiga da sauran rashin tsaro a 2023.
Asali: Legit.ng