Yanzu Fa Najeriya Bashi Muke Karba Mu Biya Bashi, Sanusi Lamido

Yanzu Fa Najeriya Bashi Muke Karba Mu Biya Bashi, Sanusi Lamido

Tsohon gwamnan bankin CBN kuma tsohon Sarkin Kano, Sanusi Lamido Sanusi, ya bayyana cewa yanzu fa Najeriya bashi ake karba don biyan wani bashin.

Sanusi ya bayyana cewa shugabannin Najeriya na tarawa jikoki da tattaba kunne bashi.

Tsohon Sarkin yace Najeriya babu wani cigaba da take da alaman samu nan gaba.

Yace bisa ga rahoton kwamitin raba kudin kasa FAAC, jihohi yan tsiraru kadai ke iya samun kudin shigan biyan albashin ma'aikatanta.

A cewarsa, a 2022 kawo yanzu Najeriya ta biya kudin bashin N2.597 trillion amma N2.4 trillion ta samu kudin shiga.

"Hakan na nufin cewa kudin biyan bashi ya zarce kudin da muke samu. Duk kudin da gwamnati ta samu yanzu bashi ake biya da su kuma a haka ma basu isa ba, sai an ci bashi kafin a iya biyan bashi, sannan kuma a biya albashi, alawun, gine-gine ," yace

Kara karanta wannan

Wai Shan Man Fetur Muke yi: Sanusi Lamido Yace Ta Yaya Ake Shan Litan Mai Milyan 66 a Rana

Tsohon Sarkin ya bayyana hakan ne ranar Asabar a taron zuba jarin jihar Kaduna KadInvest7.0, rahoton ChannelsTV.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Sanusi
Yanzu Fa Najeriya Bashi Muke Karba Mu Biya Bashi, Sanusi Lamido
Asali: Twitter

Sanusi Lamido Yace Ta Yaya Ake Shan Litan Mai Milyan 66 a Rana

Da farko, Sanusi Lamido Sanusi, ya bayyana rashin amincewarsa da ikirarin shan man fetur lita 66m a rana da NNPC tace anayi a Najeriya.

Sanusi ya bayyana cewa ta yaya za'a rika shan wannan adadin man fetur kulli yaumin tun da ba ruwan sha bane.

Sanusi ya cigaba da Alla-wadai da kudin tallafin da ake biya idan yayi kira da a sayar da NNPC kowa ya huta saboda babakere wasu yan tsiraru ke da dukiyar Najeriya.

Asali: Legit.ng

Authors:
AbdulRahman Rashida avatar

AbdulRahman Rashida

Online view pixel