Jama’a Sun Yi Martani Bayan Ganin Bidiyon Surkulle da Tinubu Yayi Kan El-Rufai a KadInvest
- Jama’a sun dinga cece-kuce kan surkullen da Bola Tinubu yayi a taron tattalin arziki da zuba hannayen jari na jihar Kaduna karo na bakwai da ya halarta
- ‘Dan takarar kujerar shugabancin kasan na jam’iyyar APC, yace Nasir El-Rufai ya mayar da rubabben al’amari zuwa lalatacce
- Kungiyar kamfen din Tinubu ta yi martani inda tace shirmen da Tinubu yayi subul da baka ne wanda kowanne ‘Dan Adam na iya yin shi har da manyan shugabanni
Kaduna - Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ‘dan takarar kujerar shugabancin kasa na jam’iyyar APC yayi surkulle tare da shirme yayin da yake magana kan Gwamna Nasir El-Rufai na jihar Kaduna a jawabin da yayi a taron tattalin arziki da zuba hannayen jari na jihar Kaduna karo na bakwai da ya halarta.
A yayin jawabi a taron a ranar Asabar, 15 ga watan Oktoban 2022, Tinubu yace Gwamnan Kaduna ya sauya:
“Rubabben al’amari zuwa lalatacce.”
“A bayyane nake rokon Gwamna El-Rufai da kada ya tafi neman karin digiri ko digirin digirgir da sauransu.”
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
- Tsohon Gwamnan Legas din yace.
“Ba zamu bar ka ka tsere ba. Hangen nesanka, kirkire-kirkirenka da jajircewarka sun sauya rubabbun al’amura zuwa lalatattu wadanda suka zama dole a irin wannan lokacin kuma hakan yasa muka halarci wurin nan.”
Surkullen Tinubu a Kaduna ya tayar da kura
Captain Barbossa, @efa101 yace:
“Shin sai mun zauna mun lura ne ko kuwa? Don a gaskiya har yanzu ban fahimta ba.”
Franklin Omani, @frvnklin yace:
“Mayar da rubabbun al’amura zuwa lalatattu. ‘Yan uwa kada mu yi burus da irin wadannan alamun.”
Oke Umurhohwo, @OkeStalyf yace:
“Ku kwatanta Tinubu ya wakilci Najeriya a majalisar dinkin duniya. Oh Allah na.”
Alexander, @AlexOgunsina yace:
“Kawai a lokacin da nake tunanin zai yi jawabi mai hankali. Boom ya leaf da.”
HenryAjis, @HenryAjis yace:
“Ko dai kunne na ke min ciwo ne? Mayar da rubabben lamari zuwa lalatacce. Oh ni.”
Sanusi II ya Sanar da Tinubu Cewa Bashi da Jam’iyyar Siyasa, Najeriya ce a Gabansa
A wani labari na daban, tsohon Gwamnan babban bankin Najeriya, Sanusi Lamido Sanusi a ranar Asabar, ya sanar da ‘Dan takarar shugabancin kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu cewa bashi da jam’iyyar siyasa.
Channels TV ta rahoto cewa, Sanusi yayi wannan batun a Kaduna yayin da ake gudanar da taron shekara shekara na KadInvest wanda Cibiyar Habaka zuba Hannayen jari na jihar Kaduna ke shiryawa
Asali: Legit.ng