Shugaban Hafsun Tsaro Ya Gargadi Ortom da Akeredolu Game da Siyan AK-47 Ga ’Yan Banga
- Wasu gwamnoni a Najeriya na duba yiwuwar fara ba 'yan banga bindigogi AK-47 domin dakile rashin tsaro
- Gwamnatin Najeriya ta sha bayyanawa karara cewa, ba daidai bane jihohi su mallaki makamai masu sarrafa kansu
- Ana yawan samun hare-hare da tashe-tashen hankula a Najeriya, lamarin dake sanya nemo mafita ga rashin tsaro
Abuja - Lucky Irabor, shugaban hafsun tsaro a Najeriya ya ce babu jihar da gwamnati ta ba ikon mallakar makamai masu sarrafa kansu musamman ga 'yan banga.
Ya bayana hakan ne a wata hira a ranar Juma'a da manema labarai bayan wani taron majalisar tsaro na kasa da aka gudanar a Abuja.
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya jagoranci zaman da aka yi, inji rahoton jaridar TheCable.
Nnamdi Kanu: Majalisar Tsaron Najeriya Ta Yi Karin Haske Kan Shugaban IPOB, Ta Bayyana Mataki Na Gaba
Gwamnoni na yunkurin ba 'yan banga bindiga AK-47
Da yake kaddamar da zubin farko na jami'an tsaron da jiharsa ta samar a watan Agusta, gwamna Samuel Ortom ya ce zai samar da makamai masu sarrafa kansu ga wadannan 'yan bangan.
DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka
A nasa bangare, gwamna Rotimi Akeredolu na jihar Ondo a watan Satumba ya ce, zai yi kokarin samarwa 'yan bangan Amotekun dake jiharsa bindiga.
Da yake martani ga wadannan maganganu, Irabor ya ce, gwamnatin tarayya ne ke da alhakin ba da izinin amfani da bindiga, misali AK-47, rahoton SaharaReporters.
A cewarsa:
"Makamai sun kasu ne gida biyu. Kuna da makamai masu sarrafa kansu da kuma wadanda ba masu sarrafa kansu ba, wadanda wasun ku na da shi idan kuka nemi lasisin mallakarsu."
Daga nan ya bayyana cewa, idan dai makami mai sarrafa kansa, to tabbas babu jihar da gwamnati ta ba damar mallaka.
Daga karshe ya shaidawa jihohi cewa:
"Don haka, ba za ku tambayi abin da baku da ikon mallaka ba."
Gwamnatin Tarayya Kadai Ba Za Ta Iya Rike Jami'o'i Ba, Iyaye Ya Kamata Su Fara Tallafawa, Inji Gwamna Inuwa
A wani labarin, gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya na jihar Gombe ya bayyana cewa, gwamnatin tarayya kadai ba ta da karfin iya rike jami'o'in kasar, Channels Tv ta ruwaito.
Ya kuma bayyana cewa, akwai bukatar iyaye da sauran masu ruwa da tsaki suke shiga lamarin domin tabbatar da tafiyar da makarantu cikin kwanciyar hankali.
Gwamnan ya bayyana hakan a ranar Juma'a jim kadan bayan da kungiyar ASUU ta ayyana janye yajin aikin da ta shafe watanni takwasi tana yi a kasar.
Asali: Legit.ng