Babban Goro: ‘Dan Sanata Gumel Yayi Wuff da Diyar Sanata Ndume, Hotunan Daurin Aure Sun Bayyana

Babban Goro: ‘Dan Sanata Gumel Yayi Wuff da Diyar Sanata Ndume, Hotunan Daurin Aure Sun Bayyana

  • A yau Juma’a an daura auren Muhammad Abdullahi Gumel, ‘dan Sanata Gumel da Kaltume Muhammad Ndume, Diyar Sanata Ndume a Masallacin kasa dake Abuja
  • Kamar yadda hotunan daurin auren suka bayyana, Bola Ahmed Tinubu, Sanata Kashim Shettima, Gwamna Yahaya Bello, Gwamna Badaru, Sanata Barau Jibril duk sun halarta
  • Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan, shi ne ya kasance waliyyin ango a auren ‘ya’yan Sanatocin da aka daura a ranar 14 ga watan Oktoban 2022

FCT, Abuja - Jiga-jigan kasar nan da suka hada da gwamnoni, ‘yan majalisa da fitattun ‘yan siyasa a yau sun taya Sanata Gumel da Sanata Ndume murnar aurar da ‘ya’yansu da suka yi a masallacin kasa dake Abuja.

Mohammed Abdullahi Gumel, ‘dan Sanata Gumel ya auri Kaltume Mohammed Ndume a Daurin auren da aka yi ranar Juma’a, 14 ga watan Oktoban 2022 a Abuja.

Kara karanta wannan

Zamfara: Sunayen Kananan Hukumomi 3 da Matawalle ya Garkame, Ya Hana Tarukan Siyasa

Daurin Aure
Babban Goro: ‘Dan Sanata Gumel Yayi Wuff da Diyar Sanata Ndume, Hotunan Daurin Aure Sun Bayyana. Hoto daga The Senate President - Nigeria
Asali: Facebook

Kamar yadda shugaban majalisar dattawa, Sanata Ahmad Lawan ya bayyana, shi ya kasance waliyyin ango yayin da manyan ‘yan siyasa da masu mulki suka halarci daurin auren.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A hotunan daurin auren da suka bayyana, an ga Ahmed Bola Tinubu, ‘dan takarar kujerar shugabancin kasa karkashin jam’iyyar APC, Sanata Ahmed Lawan, shugaban majalisar dattawan Najeriya, Gwamna Muhammad Badaru na jihar Jigawa da sauransu.

A wallafar da Sanata Ahmed Lawan yayi a shafinsa na Facebook, ya bayyana cewa:

“Shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan ya halarci daurin auren Muhammad Abdullahi Gumel, ‘dan Sanata Gumel da Kaltume Muhammad Ndume, diyar Sanata Ndume a Masallacin kasa.
“Yayin da shugaban majalisar dattawa ya kasance waliyyin ango, sauran sun hada da Gwamna Yahaya Bello, Gwamna Muhammad Badaru, Sanata Kashim Shettima, Ahmed Bola Tinubu, Honarabul Monguno Mohammed Tahir da Sanata Barau Jibril duk baki ne.”

Kara karanta wannan

Atiku Abubakar Ya Kinkimo Manya 3 Domin Su Lallabi Wike Ya Marawa PDP baya

Hotuna da bidiyo: Alkawari ya cika, an daura auren 'Yaradua da Yacine kan sadaki sisin gwal 24

A wani labari na daban, 'Dan tsohon shugaban kasar Najeriya, Umaru Musa Yar'adua, Shehu Yar'adua ya yi wuff da Yacine Muhammad Sheriff a Maiduguri dake jihar Borno a yau Asabar, 23 ga watan Yulin 2022.

An daura auren a gidan Sheriff wanda yake kusa da barikin Giwa kuma ya samu halartar shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda ya samu wakilci daga ministan sufurin jiragen sama, Hadi Sirika, Gwamna Babagana Umara Zulum da takwarorinsa na jihar Kebbi da Jigawa.

Asali: Legit.ng

Online view pixel