Majalisar Zartaswar ASUU Za Ta Kwana Tana Tattaunawa Kan Yajin Aiki

Majalisar Zartaswar ASUU Za Ta Kwana Tana Tattaunawa Kan Yajin Aiki

  • Gwamnatin Najeriya na ci gaba da kai ruwa rana da kungiyar ASUU don kawo karshen yajin aikin da suke yi
  • Majalisar zartaswar kungiyar ASUU za ta yi zaman tattaunawa don yanke shawari kan dawowa bakin aiki
  • Daliban jami'o'in gwamnatin a Najeriya na ci gaba da koka zaman gida da suke yi na tsawon watanni

FCT, Abuja - Tattaunawar majalisar zartarwar kungiyar malaman jami'a (ASUU) za ta guda a daren yau a babban birnin tarayya Abuja, inji rahoton Punch.

Ganawar, wacce manyan kungiyar ta ASUU ce za su tattauna a cikinsa zai kawo shawarin karshe ne kan yiwuwar janye yajin aikin da kungiyar ta dade tana ciki.

Majalisar zartaswar ASUU za ta yi ganawar karshe kan matsayar yajin aiki
Majalisar Zartaswar ASUU Za Ta Kwana Tana Tattaunawa Kan Yajin Aiki | Hoto: vanguardngr.com
Asali: UGC

Da take zantawa da wakilin Punch a Abuja, wata majiya ta shaida cewa:

Kara karanta wannan

Yanzu-Yanzu: Kotun Daukaka Kara Ta Sallami Shugaban IPOB, Nnamdi Kanu, Ta Kallubalanci Hukuncin Babban Kotu

"Za mu gana a yau kuma kwana za a yi domin mu samu isasshen lokacin yanke shawarin karshe."

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin da aka tambaye ta ko kungiyar za ta janye yajin aiki, majiyar ta ki yin bayani a kai, NairaMetrics ta ruwaito.

Matakin yajin aikin ASUU da halin da ake ciki

Idan baku manta ba, kungiyar malaman jami'a a Najeriya sun shiga yajin aiki tun watan Fabrairun 2022 a jami'ar Legas.

Gwamnatin Najeriya ta kai ruwa rana da kungiyar, lamarin da har yanzu ba a gama samun mafita mai dorewa ba tukuna.

Kungiyar ASUU ta bukaci gwamnatin Najeriya da ta cika yarjejeniyar da ta shiga da kungiyar a 2009, ta habaka jin dadin aikin jami'a tare da biyan mambobin ASUU alawus-alawus da take bin gwamnatin.

Ministan kwadago na Najeriya, Chris Ngige ya maka kungiyar ASUU a kotu bayan kai ruwa rana don ganin an warware lamarin yajin.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Jerin Yan Takarar Shugaban Kasar Najeriya Da Suka Yi Rajista Da Satifiket Din WAEC/SSCE Kacal

Kotun ma'aikata ta umarci ASUU ta janye yaji, amma kungiyar ta tubure ta kai maganan gaba, inda nan ma aka sake umartar da ta gaggauta komawa bakin aiki.

Rassan ASUU a jami'o'in gwamnatin sun yi zama makon nan don yanke shawarin komawa bakin aiki.

Budurwa Ta Kai Kaninta Jami'a Cotonou, Ta Yi Masa Rijistar N210k

A wani labarin, bidiyon wata budurwa 'yar Najeriya da ta yiwa kaninta rajistar makaranta a jami'ar Cotonou ya yadu a intanet, jama'a da dama sun tofa albarkacin bakinsu.

A cewar budurwar, kungiyar malaman jami'o'i ta ASUU ba za ta hana kaninta kammala karatu ba duk da cewa ba za su janye yajin aiki ba.

Ta ce ita da kaninta nata sun hau babur ne daga Legas ta hanyar Idi-Iroko, suka hau mota har dai suka shiga kasar ta Benin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel