An Kama Wasu 'Yan Jamhuriyar Kamaru 2 da Kokon Kan Dan-Adam a Jihar Adamawa
- Rundunar 'yan sanda ta bayyana kame wasu mutane da ake zargi sun sato kokon kan dan adam daga kasar Kamaru
- Bincike ya nuna sun zo Najeriya ne domin siyar da kasusuwan ga wani dan Najeriya a jihar Adamawa
- Hukumar 'yan sanda ta bayyana matakin da take dauka kan wannan lamari mai ban mamaki da ya faru
Jihar Adamawa - Jami'an 'yan sanda a jihar Adamawa sun kama wasu mutum biyu dauke da kokon kan dan adam da wasu kasusuwan da suka sato.
Hakazalika, rundunar ta kama wani da ake zargin shi zai sayi wadannan kayayyaki, Dauda Yakubu da aka ce mai sana'ar acaba ne da kuma wata mata da ake zargin tana da hannu a lamarin.
Mutanen biyu da aka kama sune Nodji Kodji da Raji Silver a kauyen Garware dake karamar hukumar Furore a jihar ta Adamawa.
Jaridar Daily Trust ta tattaro cewa, mutum biyun da ake zargi an kama su ne a ranar 11 ga watan Oktoba kuma sun taho ne daga Cholli, wata alkarya dake karkashin jamhuriyar Kamaru mai makwabtaka da Najeriya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Yadda suka kulla harkallar siyar da kasusuwan
Da suka sha matsa, sun kada baki sun ce tabbas su suka zo da kasusuwan daga Kamaru, kuma sun tono ne daga wani kabari a can don siyarwa Dauda a kan kudi CFA na Faransa miliyan 5.
Sun kuma shaida cewa, da suka kawo kasusuwan ga Dauda domin ya saya, sai yace ya fasa, daga nan suka fara neman mai saye, inda a cin wannan halin aka kwamushe su.
Mai magana da yawun 'yan sanda a jihar, SP Suleiman Yahaya Nguroje ya ce, jami'an tsaro ne suka kama wadanda ake zargin a lokacin da suke sintirin yau da kullum a yankin.
Jami’an Hisbah Sun Kama Mata Masu Yawan Gaske Saboda Kwankwadar Barasa Da Karuwanci A Wata Jihar Arewa
Da yake gabatar da wadanda ake zargin, Nguroje ya ce wata tawaga karkashin CSP Usman Jaroyel ne ta kamo su, inda ya kara da cewa, wannan babban aiki ne da hukumar 'yan sandan jihar ta yi.
Ya kuma ce, dukkan wadanda ake zargin sun amsa cewa, sun sato kasusuwan ne daga kaburbura a wani yankin Kamaru, rahoton SaharaReporters.
Hakazalika, ya ce kwamishinan 'yan sandan jihar, A.K Akande ya ba da umarcin cewa, a mai da wadanda ake zargin zuwa shashen binciken manyan laifuka domin gudanar da cikakken bincike.
Daga karshe ya shawarci a ke zuba ido sosai kan makabartu don kiyaye faruwar irin wadannan lamurra.
'Yan Sanda Sun Dura Kan Gungun 'Yan Fashin Da Suka Yi Mummunan Barna a Abuja
A wani labarin, rundunar 'yan sanda a babban birnin tarayya Abuja ta dura kan wani gungun 'yan ta'addan da ake zargin su suka yi fashi a wani shagon magani dake yankin Maitama a birnin tare da sace wata mota 'Prado'.
A baya rahoto ya bayyana yadda 'yan ta'adda suka zo da makamai tare da yin mummunan fashi a shagon maganin hadi da kashe wani mutum da ya yi kokarin kawo musu tsaiko a yunkurinsu na sace mutane.
A ranar Alhamis 13 ga watan Oktoba, kwamishinan 'yan sandan FCT, Sunday Babaji ya gabatar da wani da ake zargin yana daga cikin wadanda suka aikata barnar, Daily Trust ta ruwaito.
Asali: Legit.ng