Ana Zargin Sojoji Da Mamaye Wani Yanki A Enugu, Sun Kone Gidaje Da Dama
- Ana zargin jami'an sojoji da kai mamaya wani yanki na garin Mgbowo da ke karamar hukumar Awgu a jihar Enugu
- An tattaro cewa sojojin da ba a san dalilinsu na kai farmakin ba sun kona gidaje da dama
- Sun kai harin ne da sassafe inda suka ta harbi a sama lamarin ya sa mazauna yankin tserewa cikin dazuzzuka
Enugu - Rahotanni sun kawo cewa dakarun sojoji sun farmaki wani yanki na garin Mgbowo da ke karamar hukumar Awgu a jihar Enugu.
Sahara Reporters ta rahoto cewa lamarin ya haifar da rudani da fargaba a tsakanin al’umma yayin da mazauna yankin suna tsere cikin dazuzzuka mafi kusa.
Koda dai ba a bayyana dalilin farmakin ba; an tattaro cewa sojojin sun kona akalla gidaje guda biyar a yankin.
Wasu majiyoyi a kauyen sun bayyana cewa sojojin sun bi ta tsohuwar hanyar Enugu-Portharcourt sannan suka shiga kauten Amaeta Mgbowo ta makarantar sakandare na mata, rahoton Nigerian Tribune.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani mazaunin garin, Clement Ogonna ya fada ma Sahara Reporters cewa al’ummar kauyen sun wayi gari da karar harbi, wanda yace suna ta dira kan rufin kwano kamar saukar ruwa.
Ya ce:
“Yayin da al’ummar kauyen ke gudun tsira, sojojin sun yunkura zuwa harabar Urulor a unguwar Okegu sannan suka kona gidaje.
“Bayan sun kona wani gini a unguwar Okegu, sai suka garzaya unguwar Ogudu inda suka kona gidaje uku kafin suka koma Isingwu.
“Yanzu haka da muke magana, sojoji na kona gidaje a Isungwu; kana iya hango hayaki yana tashi a sama.”
Ya ci gaba da cewa babu wanda zai iya cewa ga dalilin sojojin na kai masu farmaki.
Yadda Matar Malamin Addini, Yaransa 2 Da Kanne Mata 2 Suka Yi Mutuwar Ban Mamaki
A wani labarin, an tsinci matar wani malamin addini mai suna Adolphus Odo kwance a mace tare da yaranta biyu da kuma kannenta biyu a Amutenyi, da ke Obollo-Afor, karamar hukumar Udenu ta jihar Enugu a ranar Asabar.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa karar kararrawar agogo ce ta ankarar da makwabta inda suka fasa kofar kawai sai suka tsinci mutanen su biyar kwance babu rai a jikinsu.
Da yake tabbatar da lamarin, shugaban karamar hukumar, Solomon Onah, ya ce labarin ya jefa yankin karamar hukumar cikin alhini.
Asali: Legit.ng