An Kama Matar Da Ta 'Sace' Tagwaye Bayan Mahaifiyarsu Ta Ki Sayar Mata Da Su
- Jami'an hukumar yaki da fataucin mutane a Najeriya, NAPTIP, sun kama wata mata yar shekara 49 kan zargin 'satar' tagwaye
- Mrs Augustina Ikyor ta shiga hannu ne bayan korafi da mahaifiyar tagwayen ta yi na cewa ta tafi mata da yara da sunan tallafi bayan ta ki yarda ta sayar da su
- Bai Gloria Iveren, kwamandan hukumar NAPTIP na Makurdi ta gargadi al'umma su rika taka tsantsan da mutanen da za su karbar yara da sunan tallafi
Benue - Hukumar hana fatauci mutane, NAPTIP, reshen Makurdi ta kama wata mata yar shekara 49, Mrs Augustina Ikyor, kan mallakar wasu tagwaye a jihar, rahoton Nigerian Tribune.
Kwamandan hukumar na shiyyar, Bai Iveren, cikin wata sanarwa, ta ce mahaifiyar tagwayen ta yi ikirarin cewa wacce ake zargin ta kwace jariran ne daga wurin ta.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Wani sashi na sanarwar ya ce:
"Mun samu kiran neman dauki daga wata mahaifiyar tagwaye yar shekara 22, wacce ta yi ikirarin cewa wata mata da bata santa sosai ba ta yaudare ta, ta karbe mata yaranta yan wata biyu.
"Ta ce da farko matan ta nemi ta sayar mata da tagwayen tunda an kore ta daga inda ta ke zaune.
"Duk da ba ta amince da hakan ba, amma da sunan tallafa mata, matar ta karbi tagwayen ta kai su wani wurin da ba a sani ba.
"Jami'an hukumar sun yi gaggawar daukan mataki a lamarin suka kai samame, suka kama wata Mrs Augustina Ikyor, 49, da tagwayen (namiji da mace). Mahaifiyar da yayan suna wurin hukuma."
Kwamandan ta yi kira ga mutane su yi takatsantsan da wadanda ke yaudarar mata musamman masu yaya ba tare da aure ba su sayar musu da yayansu da sunan taimako.
An Kama Wata Mata Ta Sace Yara 3 a Borno Zata Tafi Da Su Legas
A wani rahoton, hukumar yan sanda a jihar Borno ta bayyana wata mata mai shekara 46, Insa Henshaw, ranar Alhamis, 25 ga Agusta kan laifin satar yara uku zata gudu da su jihar Legas.
An damke matar ne a tashar mota, rahoton HumAngle.
A cewar yan sanda, an damketa ne makonni uku da suka gabata lokacin da aka ganta tana kokarin hawa motar da yaran.
Asali: Legit.ng