"Osinbajo Ne Uban Kiristocin Najeriya", Wurinsa Kadai Za Mu Iya Zuwa Ya Share Mana Hawaye, Rabaran Ali Aba

"Osinbajo Ne Uban Kiristocin Najeriya", Wurinsa Kadai Za Mu Iya Zuwa Ya Share Mana Hawaye, Rabaran Ali Aba

  • Most Rabaran Oliver Ali Aba, zababben shugaban cocin Methodist ta Najeriya ya kai wa mataimakin shugaban kasa Osinbajo ziyara
  • Yayin ziyarar, babban malamin addinin ya kwatanta Osinbajo a matsayin 'uban dukkan kiristocin Najeriya' yana mai cewa wurinsa suke zuwa ya shara musu hawaye
  • Hakazalika, Aba ya jinjinawa halayen kirki na Osinbajo da ya ce zai yi koyi da su kuma ya yabi gwamnatin Shugaba Buhari kan nasarorin da ta samu

Abuja - Zababben Prelate na cocin Methodist ta Najeriya, Most Rabaran Oliver Ali Aba, ya bayyana mataimakin shugaban kasa, VP, Yemi Osinbajo a matsayin wanda kirista za su iya kai kukansu wurinsa idan suna cikin damuwa.

Ya yi wannan jawabin ne a lokacin da Osinbajo ya karbi bakuncin wata tawaga da Cocin Methodist karkashin jagorancin zababben Prelate din a ranar Talata a fadar Aso Villa, rahoton Channels Television.

Kara karanta wannan

Atiku da Okowa Zasu Fitar Da Najeriya Daga Kangin Talauci, Kwamitin Kamfen PDP

Osinbajo
"Osinbajo Ne Mahaifin Kiristocin Najeriya" In Ji Babban Rabaran Na Cocin Methodist. Hoto: Channels Television.
Asali: Facebook

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Wata sanarwa da Laolu Akande, hadimin Osinbajo ya fitar, ta ambaci malamin addinin na cewa VP din shine "Uban kiristocin Najeriya" kasancewarsa kirista mai rike da mukami mafi girma a kasar.

Ya shaidawa VP din cewa:

"Kai ne uban kiristoci a Najeriya, kai ne kadai za mu iya zuwa mu kawo kukan mu a lokacin da muke cikin bukata.
"Akwai abubuwa da dama da za a iya koya daga gare ka, kan-kan da kai, jajircewa a gwamnati, da himma wurin hidimtawa mutane. Na koyi dukkan wannan halayen kuma zan maimaita su a jagorancin Cocin Methodist. Na yi imanin zan daukaka cocin zuwa babban mataki idan na yi koyi da halayenka."

Most Rabaran Aba, wanda tawagarsa ta taho don yi wa VP din bayani kan taronsu na Legas da za a yi a wata mai zuwa, ya kuma jinjinawa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari bisa nasarorin da ta samu.

Kara karanta wannan

Sanatan Kano Ya Bayyana Ainahin Wanda Osinbajo Yake Goyon Baya A Zaben Shugaban Kasa Na 2023

Osinbajo mayaudari ne, ko Yesu zai iya yaudara: Kungiyar Kiristocin Arewa

A wani rahoton, Kungiyar Kiristocin Arewa watau Northern Christians Movement (NCM) ta gargadi yan siyasa da Malamai su yi hattara da mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo.

Kungiyar tace ta yi hasashen cewa Osinbajo mutum ne wanda zai yaudari duk wanda ya taimakesa.

Wannan ya biyo bayan ayyana niyyar takarar kujerar shugaban kasa da Farfesa Yemi Osinbajo yayi ranar Litinin, rahoton Infong.

Asali: Legit.ng

Online view pixel